Boko Haram Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago A Maiduguri

Manoma biyu Yan kungiyar Boko Haram suka kashe a kauyen Kuwa-Yangewa dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Mai rikon muƙamin kwamandan rundunar sojan Najeriya ta 7, Abdulmalik Biu ya ce yan ta’addar sun kai harin ne kan wasu rukunin nutane dake kalen ragowar amfanin gona a gonaki inda suka kashe biyu daga ciki.

Biu ya bayyana cewa sojoji da aka tura yankin sun garzaya ya zuwa wurin da abin ya faru lokacin da daya daga cikin matan da abin yafaru akansu ta kai musu rahoto.

Kwamandan ya ce ya ziyarci wurin da aka kai harin domin duba halin da ake ciki inda ya kara da cewa tuni komai ya cigaba da tafiya kamar yadda yake a baya.

“Wasu mutane sun tafi gona kuma mayakan ƙungiyar Boko Haram sun kai musu hari sun yanka wani dattijo da kuma wani matashi,”ya ce.

“Matar dattijon ce ta yi gudu ta zo ta fadawa sojoji inda suka garzaya wurin domin ceto su.maharan sun gudu lokacin da suka hango sojojin suna tahowa.

“Mutane biyu kadai aka kashe a harin babu wanda kuma aka lura an sace a harin.”

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*