Connect with us

Kannywood

Idan Ba Ku Zabi Buhari A 2019 Ba, Wallahi Za Kuyi Nadama -Adam A Zango Ga ‘Yan Najeriya

Published

on

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya baiwa ‘yan Najeriya shawara akan sake zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari a zaben shekarar 2019 me zuwa.

Adamu a cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinshi na sada zumunta ya bayyana cewa, tunda ya fara sana’arshi babu wani dan siyasa me ci ko wanda ya sauka da ya taba taimakamai da miliyan daya ko dubu dari, neman na kanshi yake tukuru.

Ya kara da cewa, yana so ya baiwa ‘yan Najeriya shawara kuma zai yi wannan maganane bil hakki har cikin zuciyarshi ba dan wani ko wata ba.

Yace idan ‘yan Najeriya suka yadda Buhari ya fadi mulki to zasu yi dana sani amma idan suka sake zabenshi zasu dara har zuwa ranar da zai sauka daga mulki.

A karshen maganarshi yace, idan kunne yaji..

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook

Advertisement

Trending