Wata Lauya A Ta Yanke Mazakutar Mijinta, Ta Buge Da Hauka

Wata lauya ta kashe mijin ta ta hanyar yanke masa al’aura sannan ta saka su cikin hannun sa na dama, a rukunin gidajen Diamond dake Sango-Tedo a Legas.
‘Yan sanda sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30 na safiyar jiya Alhamis, inda suka yi nuni da cewar abin babu kyan gani.
Marigayin, Otike Odibi, dan asalin jihar Delta, wanda shi ma lauya ne, ya auri matar sa, Udeme Odibi, ‘yar asalin jihar Akwa Ibom, shekaru uku da suka wuce. Lauyar da ta yanke mazakutar mijinta Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar, Legas SP Chike Oti, ya ce DPO din su dake Ogomah a Ajah aka fara kira tare da sanar da shi cewar matar Mista Otike Odibi ta kashe shi a gidan su dake unguwar Sango-Tedo.
“Bayan samun wannan kira ne sai ya ya jagoranci tawagar jami’an sa inda suka je suka iske Mista Odibi cikin jini male-male, an farke cikin sa har ta kai ga ana ganin hanjin sa. Bayan haka kuma ga shi an cire masa mazakuta an saka a hannun sa na dama,” a cewar kakakin ‘yan sanda Chike Oti.
Sai dai kafin zuwan jami’an tsaro uwargida Udeme ta yi kokarin kashe kan ta, amma hakan ba ta yiwu ba.
Yanzu haka tana asibiti domin duba lafiyar ta.
Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, CP Edgal Imohimi, ya bukaci sashen kwararru a bangaren binciken kisa na hukumar ‘yan sanda da gudanar da binciken kwakwaf a kan batun kisan.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*