Ronaldo Ya Zabi Lambar Da Zai Goya A Manchester United

Wani rahoto mai yankan kauna da shafin jaridar Daily Trust ta ruwaito ya bayyana cewa, fitaccen dan wasan kwallon kafar nan watau Cristiano Ronaldo, tuni ya zaɓi Lambar da zai goya idan ya koma kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
A cewar Don Balon, wata kafar watsa labarai a can kasar Andalus watau Spain, Ronaldo ya bukaci goya sananniyar lambar da ya saba goyawa watau Lamba 7.Cristiano wanda ya goya wannan Lamba har na tsawon shekaru shidda a Manchester United kafin ya koma Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid a shekarar 2009 ya sake bayyana muradin sa akan wannan Lamba.
Sai dai hanzari ba gudu ba, fitaccen dan wasan nan da Manchester United ta sayo daga Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal watau Alexis Sanchez, shike sanye da wannan Lamba tun watan Janairun da ya gabata.
Jaridar ta Don Balon ta yi ikirarin cewa, babban mai horas da yan wasa a kungiyar Manchester United, Jose Mourinho, ya bayyana cewa dole Sanchez ya mika wannan Lamba ga Ronaldo matukar yana son zaman sa a kungiyar.
Rahotanni sun bayyana cewa, zabi dai a halin yanzu ya rage ga Sanchez dan asalin Kasar Chile na hakura da wannan Lamba ko kuma ya kama gaban sa wajen neman wata sabuwar Kungiyar.
NAIJ.com ta fahimci cewa, tuni dai hasashe ya bayyana cewa Cristiano Ronaldo na neman barin farfajiyar wasanni ta Santiago Bernabue inda yake baje basirar sa ta tamola a kungiyyar kwallon kafa ta Real Madrid.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*