Rikici Ta Barke A Majalisar Wakilai

Zauren majalisar wakilai ya kaure da hayaniya yayinda mambobi suka ki aminta da kaddamar da ranar 12 ga watan Yuni a matsayin ranar Demokradiyya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi.
Jaridar Punch ta rahoto cewa wasu yan majalisan sun goyi bayan hakan yayinda wasu suka bukaci shugaban kasa ya janye hukuncin.Kakakin majalisa Yakubu Dogara na kokarin daidaita hayaniyan domin ci gaba da muhawaran.
Wasu daga cikin yan majalisan sun ja da karramawar da aka ba Moshood Abiola, mutumin da ya lashe zaben 12 ga Yuni na 1993 wanda sojoji suka soke.
A baya NAIJ.com ta rahoto cewa kungiyar kare muradun Yarbawa zalla ta Afenifere ta yabawa Buhari kan wannan mataki da ya dauka na girmama Abiola tare kuma da canja ranar dimokradiyya sai dai kuma kungiyar ta nuna shakku kan manufar siyasa da Buhari ke son cimma wa.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*