Connect with us

Kannywood

Inasa Wadannan Kayan Ne Don Jawo Hankalin Masu Kallo Na – Adam A Zango

Published

on

Shahararren jarumin nan na kannywood kuma mawaki, Adam A.Zango yayi Magana akan korafin da jama’a keyi game da irin kayan da yake sanyawa a cikin bidiyon wakokin shi.
A wata hira ta musamman wanda ya wallafa a shafin sa na zumunta, Zango ya bayyana cewa ya na sanya irin kayan zamanin ne domin janyo hankalin jama’a wajen kallon wakokin yan arewa.
Yace dabarar yin haka shine domin jawo hankalin samari da yan mata masu kallon wakoki kasar waje da na kudancin kasa zuwa kallon nashi.
Ya kara da cewa mafi yawanci mabiyan sa masu bibiyan wakokin turawa da na india basu san kalamai da mawakan ke furtawa a cikin wakokin su kuma mafi yawanci kalamai ne wanda bata dace ba wanda bahaushe kuma musulmi ya dinga furtawa.
A cewar sa yana kokari wajen rera wakoki cikin yaren hausa kuma ya sanya mata kida irin ta zamani kuma ya sanya kayan zamani a cikin ta domin janye hankalin jama’a zuwa kallon nashi.
Ya jadadda cewa hakan yunkuri ne na janyo hankulan mutanen arewacin kasar wajen yin alfahari da mawakan yankinsu.
Source :naij hausa

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook

Advertisement

Trending