Connect with us

Siyasa

Gwamnan Jihar Bauchi Ya Maye Gurbin Mataimakin Gwamnansa Dayayi Murabus

Published

on

Labarin da muke samu da dumin sa na nuni ne da cewa Gwamnan jihar Bauchi dake a shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya nada Alhaji Audu Sule Katagum a matsayin sabon mataimakin sa.
Kamar dai yadda muka samu, Gwamnan ya bayyana wannan nadin ne lokacin da yake ganawa da wasu masu ruwa da tsaki a gwamnatin sa a gidan gwamnatin jihar.
NAIJ.com ta samu cewa shi dai Alhaji Audu Sule Katagum an nada shi ne domin ya maye gurbin tsohon mataimakin gwamnan Injiniya Nuhu Gidado da yayi murabus a watan jiya.
A wani labarin kuma, Babban jakadan kasar Ghana a Najeriya Mista Rashid Bawa ya nesanta kasar sa da kalaman da aka ruwaito wai cewa tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce shugaban kasar Ghana Nana Akuffo-Addo ne ya fada game da harkar tsaron Najeriya.
Da yake karin haske game da lamarin, jakadan kasar Ghana din ya fada a ranar Juma’ar da ta gabata cewa tsohon shugaban kasar ya datsi kalaman shugaban kasar ta Ghana ne amma ba haka yake nufi ba.
Source :naij hausa

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook

Advertisement

Trending