Gwamnan Jihar Bauchi Ya Bayyana Sabon Mataimakin Sa

Biyo bayan ritayar tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Bachi Nuhu Gidado yanzu haka wata majiya mai karfi daga fadar Gwamnatin ta bayyana cewa tuni Gwamnan jihar Mohammed Abdullahi Abubakar ya mika sunan shugaban Ma’aikata na jihar Audu Sule Katagum ga Majalisar Dokokin jihar domin tabbatar da shi.
Sai kuma Majalisar Dokokin jihar ta tafi hutu, amma bisa bayanan da majiyarmu ta samu ya nuna cewa ‘yan Majalisar zasu katse hutun nasu gami da dawowa bakin aiki na wani dan taki domin su fara zama a yau Juma’a don duba wasikar da Gwamnan jihar ya tura musu dake kunshe da wanda yake son maye gurbin tsohon Mataimakin nasa da shi.
Kamar yadda Jaridar Tribune ta rawaitoTsohon Mataimakin Gwamnan Nuhu Gidado ya dai sauka ne a Larabar makon da ya gabata bisa radin kansa.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*