Dalilin Dayasa Sakataren Jam'iyyar APC Ya Aje Aikinsa

Da sanadin shafin Jaridar Daily Trust mun samu wani sabon rahoto a ranar Asabar din da ta gabata cewa, Sakataren kwamitin shirye-shiryen gudanar da gangamin jam’iyyar APC, Sanata Benjamin Uwajumogu ya yiwa kujerar sa murabus.
A ranar Asabar din da ta gabata ne Uwajumogu ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin Kasar nan na Abuja.
Sakataren ya shaidawa maname labarai cewa ya yanke wannan shawara ne a sakamakon wasu dalilin na karan kansa domin fuskantar wasu al’amurra da suka shafi ahali da dangin sa.
Sanata Uwajumogu ya kuma bayyana cewa ya aikata hakan ne musamman domin kwantar da tarzoma da rikici da za ta haifar da ci gaba cikin jam’iyyar APC a mahaifar sa ta Jihar Imo.A sanadiyar haka ne Sakataren ya yi godiya ga shugaban jam’iyyar na Kasa, Cif John Odigie-Oyegun da kuma sauran jiga-jigan jam’iyyar dangane da wannan dama da suka ba shi na yiwa jam’iyyar sa hidima.
Ya kuma yabawa dukkanin ‘yan jam’iyyar da suka mara ma sa baya yayin da yake fatan nasara da alheri wajen tabbatar da gangamin jam’iyyar da aka kayyade ranar 23 ga watan Yuni domin gudanarwa.
Uwajumogu wanda ya bayyana cewa tuni shugabannin jam’iyyar su ka yi idanu biyu da wasikar sa ta murabus yayin da kuma ya watsi da jita-jitar yin almundahana da kudaden jam’iyya.
Sakataren ya tafi akan cewa ya kafa tsaftataccen tarihi sakamakon yadda ya alkinta duk wasu kudaden jam’iyyar da suka biyo ya hannun sa tun yayin da ya karbi wannan mukami.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*