Buhari Zai Riga Rana Faduwa A Zaben 2019 – Wani Malamin Addini

Wani babban malamin addinin kirista a Najeriya mai suna Fasto Gabriel Adegboye ya yi hasashen cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ba zai zarce ba a zaben da za’a yi na shekarar 2019.
Kamar yadda majiyar mu ta jaridar Nigerian tribune ta tuwaito, babban faston ya ayyana cewa ya samu wahayi ne daga ubangijin sa game da cewar wani sabon jini ne zai karbi mulki daga hannun shugaban kasar.
A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Ekiti dake zaman daya daga cikin manyan ‘yan adawar shugaban kasa Muhammadu Buhari a Najeriya watau Gwamna Ayodele Fayose ya shawarci shugaban da ya janye kudurin sa na yin tazarce ya baiwa matasa dama masu jini a jika.
Gwamnan dai ya bayyana hakan ne a dandalin sadarwar zamani na tuwita inda ya ce shekarun shugaban kasar sun wuce a ce yana mulkar ‘yan Najeriya yanzu.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*