Abinda Saraki Yace Game Da Film Din Hausa

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Bukola Saraki, ya yaba wa yan fim din Hausa da manya – manyan jiga-jigan masana’antar fim din wadanda aka fi sani da Kannywood sakamakon gudumawar da suke badawa ta fannin raya al’adun Hausa, da kuma samar da aiyuka ga dubunnan mutane a fadin kasar nan.Saraki ya yabawa ‘yan fim dinne yayin da ya karbe su lokacin da suka kai masa ziyara a jiya.
Shugaban majalisar ya sa hotunan shi tare da ‘yan fim din Hausan a shafin sa na instagram a ranar Larabar nan. Saraki ya yabawa masana’antar fim din inda yace, “Yan fim din mu na gida Najeriya sune suke na biyu a dukkanin masana’antun fim na duniya”
.Wannan ne yasa, ganawa mazan su da matan su, da masu bada umarni, da masu shirya shirye shiryen su a daren jiya ya zamo min abin farinciki.
Salisu Aliyu(Chali), Ali Nuhu, Tijjani Faraga da Maryam Habila su suka jagorance su.Ya kara da cewa wadannan mutane suna iya bakin kokarin su don habaka harshen hausa a sinima wanda miliyoyin mutane ke kallo.
“Masana’antar Kannywood ta samar da aikin yi ga miliyoyin matasa ta hanyar kayatarwa da nishadantarwa,” inji Saraki.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*