Zamu Fatattaki Karuwai Da Mashayan Giya Daga Jihar Mu – Gwamnatin Borno

Gwamnatin jihar Borno dake a shiyyar arewa maso gabashin Najeriya a karkashin shugabancin Gwamna Kashim Shettima ta baiwa dukkan gidajen karuwai da na mashaya giya wa’adin kwana uku kacal domin su kwashe tarkacen su canja wuri.
Sanarwar hakan dai ta fito ne daga wani kwamitin din-din-din da gwamnatin ta kafa mai karfi karkashin shugabancin kwamishinan shari’a na jihar, Barista Kaka Shehu Lawan da mambobin sa na hukumar ma’aikatar filaye da safiyo na jihar.
NAIJ.com dai ta samu cewa kwamitin ya bayar da wa’adin ficewar ta su ne daga unguwannin da suke zaune da suka hada da yankin Galadima da sauran unguwannin cikin garin na Maiduguri daga ranar 29 ga Mayu zuwa 2 ga watan Yuni da su tattara su bar yankunan ko kuma su fuskanci hukunci mai tsanani.
A baya ma dai mai karatu zai iya tuna cewa gwamnan jihar ya bayar da umurni ga masu shirya cacar nan ta Bet 9ja da su fice su bar jihar.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*