Zamu Cire Yan Nijeriya A Halin Da APC Ta Saka Su – PDP

Shugaban Jam’iyyar PDP na kasa Uche Secondus ya bayyana cewa Jam’iyyar su za ta ceci ‘Yan Najeriya daga mulkin APC. Secondus ya bayyana wannan ne a karshen makon da ya wuce a Garin Osun.
Mun samu labari daga Jaridun kasar nan cewa a Ranar Asabar, Jam’iyyar PDP ta gudanar da wani gangami na Yankin Kudu-maso-yammacin Kasar a filin shakatawan Nelson Mandela da ke Garin Osogbo a Jihar Osun.
Dubban ‘Yan PDP irin su tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, da Gwamna Ayo Fayose da tsohon Gwamnan Jigawa Alhaji Sule Lamido, da wasu manyan PDP a Yankin irin su Rasheed Ladojo su na wajen taron.
Uche Secondus yace Jam’iyyar adawar za ta kawo karshen wahalar da Gwamnatin Buhari ta jefa jama’a a Kasar. Wani ‘Dan takarar Gwamnan Osun Oluomo Gbenga Owolabi ya sha alwashin Jam’iyyar sa za tayi nasara a zaben Gwamna.
Source :Naij Hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*