Wata Mace Tabawa Maza Mamaki A Gasar Harbi

Wata mace soja, Cpl. Vivien Ogbuah, dake sansanin hukumar soji na 3 dake Jos ta lashe kofin gasar iya harbi na shekarar nan. Rundunar soji ta 3 dake Rukuba a Jos ne ta shirya gasar.
An kammala gasar ta tsawon kwana hudu da ta kunshi dakarun soji daga sansani daban-daban a yau, Alhamis.Bayan zama zakara a gasar harbin dakarun soji ta kowa da kowa, Vivien ta lashe gasar harbi ta mata zalla.
Da yake jawabi yayin kammala gasar, shugaban rundunar soji a jihar, Manjo Janar Benjamin Ahanotu, da Birgediya janar Aliyu Abdullahi, ya wakilta ya yabawa dakarun sojin bisa halayyar tarbiya da kwarewa da suka nuna yayin gasar.An shirya gasar ne tsakanin kananun sojoji daga barikin soji dake jihohin Filato da Bauchi.
A wata rahoton da NAIJ.com ta kawo muku “Wata lauya ta kashe mijin ta ta hanyar yanke masa al’aura sannan ta saka su cikin hannun sa na dama a rukunin gidajen Diamond dake Sango-Tedo a Legas.
‘Yan sanda sun bayyana lamarin da ya faru da misaln karfe 7:30 na safiyar yau, Alhamis, da cewar babu kyan gani.
Marigayin, Otike Odibi, dan asalin jihar Delta, wanda shi ma lauya ne, ya auri matar sa, Udeme Odibi, ‘yar asalin jihar Akwa Ibom, shekaru uku da suka wuce.Kakakin hukumar ‘yan sanda a jihar, Legas SP Chike Oti, ya ce DPO din su dake Ogomah a Ajah aka fara kira tare da sanar da shi cewar matar Mista Otike Odibi ta kashe shi a gidan su dake unguwar Sango-Tedo.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*