Wani Minista Yayi Murabus Daga Kujeranshi

Ministan ma’adinai, Dakta Kayode Fayemi, ya yi murabus daga kujeransa domin mayar da hankali kan kada mataimakin gwamnan jihar Ekiti, Olusola Eleka, a zaben jihar Ekiti da za’a gudanar ranan 14 ga Yuli mai zuwa.
Fayemi ya mika wasikar murabus dinsa ga shugaba Muhammadu Buhari ne makonni uku da suka gabata amma a yau, 30 ga watan Mayu ne zata fara aiki.
Ministan zai yi takara kujeran gwamnan jihar ne karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) bayan ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar da aka gudanar ranan 12 ga watan Mayu.
Ya lashe zaben da kuri’u 941 inda sauran masu takaran guda 31 suka fadi, wadanda suka dan tabuka wani abu sune, Segun Oni (Kuri’u 481 ), Kayode Ojo (Kuri’u 281), Olufemi Richard Bamisile (Kuri’u 179), Oluyede Oluwole (Kuri’u 121), da Aluko Daniel Olugbenga (Kuri’u 86).
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya lashi takobin cewa Fayemi ya sha kasa a zaben 14 ga watan Yuli.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*