Kunsan Gwamnan Arewa Da Ya Nemi Alfarma Gun Davido?

Mun samu labari cewa a makon can ne wani babban Gwamnan PDP a Arewacin Najeriya ya nemi alfarma wajen fitaccen Mawakin nan na Najeriya da aka sani da Davido wanda shi kuma ya amince ya yarda da abin da aka nema.
Mai Girma Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na Jihar Gombe yayi kira ga Davido wanda yake tashe a Duniya cewa yayi amfani da basirar da Allah ya ba sa domin yayi kira ga Jama’an Najeriya su karbi katin zabe mai zuwa.
Gwamna Ibrahim Dankwambo ya roki Davido yayi wata waka da za ta sa jama’a su yanki katin zabe na PVC domin ganin kowa ya kada kuri’a a zaben 2019. Gwamnan yace yana cikin masoya wannan shararren Mawakin.
Shi dai Davido tuni ya amsa wannan kira inda yace zai yi wannan waka domin ganin ya fadakar da jama’a game da karben katin na PVC. Duk an yi wannan ne a shafin Tuwita inda Davido yace zai yi abin da zai taimaki kasar sa.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*