Kungiyar Shi’a Ta Rabe Gida Biyu

Wani bangaren kungiyar Shi’a mai suna Rasulul A’azam Foundation, RAAF, a ranan asabar ta nuna goyon bayanta ga gwamnatin Najeriya sabanin bangaren Ibrahim Zakzaky masu fito na fito da gwamnati.
Sakataren kungiyar Rasulul A’azam Foundation, RAAF, Sale Zaria ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a taron bikin tunawa da Imam El Mahdi da sukayi karamar hukumar Ngoggo da ke jihar Kano.
Game da cewarsa, Rasulul A’azam Foundation, RAAF, yan zaman lafiya ne, masu zaman kansu kuma masu son hadin kan Najeriya.
Mal Sale Zaria ya yi kira ga Musulmai da mutanen Najeriya da su nisanta kansu da duk wani abu da zai tada rikicin addini da kabila a Najeriya.
Ya caccaki mabiya Sheik Ibrahim Zakzaky a kaikaice inda yace mabiya addini su nisanci tsattsauran ra’ayi da kuma fito na fito da gwamnatin da Allah ya bawa mulki.
Sale Zaria ya kara da cewa akwai banbanci tsakaninsu da kungiyar IMN ta Zakzaky duk da cewa dukkansu yan Shi’a ne.
Source :Naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*