Hadiza Gabon: Tsakanin Riya da Tarkon Shaidan

Daga Fatahu Mustapha
Wato wani babban tarko da shaidan kan daura mana akan hanyarmu ta aikata alheri, ita ce:  ta hana mu aikin lada, saboda tsoron riya. Sau da yawa mukan yi yunkurin yin abin arziki, Amma saboda tsoron kar aikin ya zama riya, sai mu fasa. Da yawanmu, mu kan fada cikin wannan tarko, har ya zamana munyi asarar lada mai gwabi, saboda kawai muna tsoron riya.
Matukar bamu yaki wannan mummunan tarko ba, to kuwa zamu zauna kullum cikin asarar samun lada mai yawa. Malamai da dama sun jawo hankalinmu akan lallai mu guji riya, cikinsu kuwa har da shehin malamin nan, AbdurRahman al Ahzari, wanda ya rubuta shahararren littafin nan mai suna: Lahillari.  To amma kuma sunyi kashedi da cewa, mu kuma lura da cewa ita riya, wani tarko ne, da shaidan kan kafawa mumini, domin hana ayyukan alheri. Dan haka kar mu yadda , tsoron riya ya hana mu aikata alheri.
Kamar yadda malam Yakubu Musa ya nuna a rubutunsa, ya kuma jawo hankalinmu, ina ga ya kamata in mun ga wani na aikata abin arziki, to mu yi kokari taimaka masa ya aiwatar, domin muyi tarayya  da shi a ladan.  Abin takaici ne, ganin yadda wasu suka tsangwami wani kyakkyawan aiki da wata baiwar Allah mai suna Hadiza Gabon  (yar fim) take yi, wai su a ganinsu wannan aiki na ta, riya ce.
Ina jiye musu tsoron kar su fada cikin Tarkon hassada, Wadda ita ce laifin da , ba kawai alhaki kake samu ba, ai har ayyukan ka na alheri ma take cinyewa.  Hassada ita ce, masifar da Allah da kansa yace wa manzon Allah ya nemi tsari da ita ” wa min sharri hasidin iza hasada”. Jin  hassada a zuciya na da sauki, Amma babbar masifar ita ce aikata ta. Domin Allah cewa yayi, “… da  sharrin mai hassada, in yayi hassadar ” shin bama tsoron aibata kyakkyawan aikin da Hadiza keyi, zai iya bayuwa zuwa ga hassada?
Akwai abin lura ga wannan, domin a wani hadisi, manzon Allah ya Umarce mu, da muyi wa mummini kyakkyawan zato.  Shin wannan hadisin bai inganta bane? Me yasa ba zamu kyautata mata zaton tana yi ne Dan Allah ba?
Babbar masifar itace, an tauye mata hakkinta a matsayinta na musulma.  Domin a hakkokin da manzon Allah ya fada na Musulmi akan Musulmi ya bayyana cewa “musulmi Dan uwan musulmi ne… kada kuyi masa keta, kada kuyi masa hassada…” Wanda duk ya soki wannan aikin alheri da Gabon take yi, ko shakka babu, ya sabawa wadannan hadisai guda biyu.  Dole ne ayi mata kyakkyawan zato, kuma a kara mata kwarin guiwar da ta cigaba da wannan kyakkyawan aiki da take.  Ina fatan malam Yakubu zamu yi amfani da raayi Initiative mu karramata, saboda a kara mata kwarin guiwa, a kuma zaburar da sauran takwarorinta yan film da su ma su ringa wannan  aikin alheri da take yi.
Waffaqanallahu

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*