Fadar Shugaban Kasa Ta Gayyaci Adam A Zango Wani Babban Taro

A iya cewa sakamakon suna da fitaccen jarumin fina finan Kannywood, Adam Zango yayi biyo bayan muhimmin rawar da yake takawa a fagen shirin fina finan Hausa, haka ya sanya idanun jama’a ya koma kansa, inda a dalilin haka ya samu karbu a ciki da wajen Najeriya.
NAIJ.com ta ruwaito a daren ranar Talata, 29 ga watan Mayu ne aka hangi jarumin Gwaska, Adam a wani babban taro da fadar shugaban kasa ta shirya, inda aka hange shi yana gaisawa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
Fadar shugaban kasa ta shirya wannan liyafar ne a bikin murnar zagayowar ranar Dimukradiyya na shekarar 2019, inda aka gayyaci fitattun jaruman fina finan Hausa da na Turanci.
A yayin wannan taro, mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci manyan jami’an gwamnatin Najeriya wajen yanka kek na murnar cikar Najeriya shekaru 19 akan turbar Dimukradiyya.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*