Duk Wanda Baida Katin Zabe Bazai Shiga Coci Ba – Inji Fasto

Limamin cocin Flock of Christ Mission, Warri, jihar Delta Bishop Simeon Okah ya sanar da cewa daga yanzu, duk wani dan cocinsa da bai mallaki katin zabe ba, “ba za’a bar shi yayi bauta ba.
”Har ila yau Fasto Okah ya kasance shine mataimakin shugaban kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria, PFN, sannan kuma yayi sanarwar ne yayinda yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar a Warri, jihar Delta.
Yace zamani ya wuce da kiristoci ke kallon siyasa a matsayin sabo.
Babu shakka yan Najeriya sun dauki al’amarin mallakar katin zabe da muhimmanci a wannan karo, domin a bayyana yadda aka kori ma’aika uku kwanan nan saboda basu da katin zabe.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*