Dino Melaye Ya Koma Jam'iyyar PDP

Labarin da ke shigo mana yanzun nan na nuna cewa sanata mai wakiltan Kogi ta yamma ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP da safen nan. Sanatan ya bayyana sauya shekarsa ne a zauren majalisa a yau.
Takaddama tsakanin Sanata Dino Melaye da gwamnatin tarayya ya fara ne tun lokacin da hukumar yan sandan Najeriya ta alanta neman Dino Melaye ruwa a jallo bisa ga zargin daukan nauyin wasu yan baranda a jihar Kogi.Hukumar shiga da ficen Najeriya ta damke Sanata Dino Melaye a babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja yayinda yake kokarin zuwa kasar Maroko.
Daga baya hukumar yan sanda suka garkameshi domin gurfanar da shi a kotu a garin Lokoja, jihar Kogi, amma sanatan ya tsallo daga cikin motan sanda kuma ya ji rauni.
Haka dai aka cigaba da kai komo tsakanin hukumar yansanda da Sanatan daga asibiti zuwa kotu. daga karshe dai kotu ta bada belinsa.
Masu sharhi sun bayyana cewa an yi masa sanatan bita da kulli ne bisa ga maganganun batancin da yake yiwa shugabancin shugaba Buhari da kuma jam’iyyar APC.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*