Dalilin Da Ya Sa Na Karbi Musulunci, Inji Uwargidan Gwamnan Jihar Ogun

Uwargidan gwamnan jihar Ogun, Olufunsho Amosun ta labarta yadda ta samu kanta cikin musulunci bayan auren ta da gwamnan, Sanata Ibikunle Amosun.
A cikin wata hira da jaridar Vanguard, uwargidan gwamnan ta ce “farkon wanda na fara bayyanawa aniya ta ta auren musulmi ita ce mahaifiyata. Farko sai ta fashe da kuka sannan ta tambaye ni ko na gayawa mahaifina wanda babban fasto ne na ce a’a.
“Amma a yau, mahaifiya ta da miji na sun zame mini manyan abokai. Wani lokacin mahaifiyata ta kan yi raha da maganar idan ta tuna.
“lokacin da na gayawa mahaifi na sai ya ce wannan abu ne na addu’a. amma ni abunda na fahimta shine, miji na  yana da matukar imani. Kuma na san miji na bai yi imani da komai ba sai Allah.”
Da aka tambaye ta ko mijin ta ya musuluntar da ita ne da karfi tsiya, uwargidan gwamnan sai ta kada baki tace “ muna zaune cikin aminci kuma muna yin abu tare. Idan lokacin Sallah ya yi zan ce wa ‘ya’ya na su tashi maza su yi sallah. Su kuma sai suce momi me ya sa ke bakya sallah tare da mu, ko baban mu ba addinin kwarai yake bi bane.
Daga nan ne na zauna na yi tunani mai zurfi, cikin kankanin lokaci na fara sallah ni ma na zama Musulma. Sauran dogon labari ne amma ni na zabi musulunci,” inji Amosun.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*