Barazanar Kwankwaso Wa Ganduje

Wakilin al’ummar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi barazanar kawar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Gandue, kamar yadda NAIJ.com ta jiyo.
Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da masoya da magoya baya a ranar Laraba 30 ga watan Mayu, inda yace ya zama wajibi kowannensu ya amshi katinsa na kada zabe.
“Ga duk mai hankali ya san akwai bukatar canza canji a jihar Kano, don haka ya zama wajibi akan kowa ya je ya amshi katinsa na kada zabe daga hukumar zabe ta kasa, ana nan ana rabawa.” Inji Kwankwaso.
Idan za’a tuna Sanata Kwankwaso ne ya yi ruwa ya yi tsaki don ganin gwamna Ganduje ya kai labari a zaben shekarar 2015, a lokacin da Gandujen ke rike da mukamin mataimakin gwamanan jihar Kano.
Sai dai dangantaka ta yi tsami ne tsakanin Kwankwaso da Gandujen ne jim kadan bayan Kwankwaso ya mika masa ragamar mulki, inda Gandujen ya bayyana cewa Kwankwaso na so ne ya dinga juya shi daga waje, abinda shi kuma ba zai lamunta ba.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*