Ali Nuhu Zai Sake Film Din Mujadala Don Tunawa Da Ahmad S Nuhu

Zuwa yanzu a iya cewa shirye shirye sun nisa matuka game da sabunta shirin shahararren Fim din nan da yayi suna a shekarun baya, watau Mujadala, sai dai abinda ya ja hankali yan kallo shi ne wanda zai maye gurbin marigayi Ahmad S nuhu.
BBC Hausa ta ruwaito Kamfanin shirya Fina finai na Mai Shadda ne zai dauki nauyin shirya wannan Fim, inda tace a ranar 10 ga watan Mayu ne zata fara nadirsa, haka zalika kamfanin ta bayyana cewar jarumi Umar M Shareef ne zai maye gurbin Ahmad.
Shi dai wannan Fim ya shahara a tsakanin yan kallo da masu bibiyan fina finan Kannywood, wanda ya kunshi taurari kamarsu Ali Nuhu, Sani mai Iska, Fati Muhammad, Abida Muhammad, Maijidda Abdulkadir da kuma Ahmad S Nuhu, wanda shine ya fitaccen jarumi a Fim din.
Majiyar Jaridar Naij ta ruwaito Ahmad ya rasu ne a shekarar 2007 sakamakon hadari da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri bayan fitowarsa daga garin Azare na jihar Bauchi inda ya gudanar da wasan Sallah.
A zamaninsa, Ahmad ya kasance jarumi mai tashe, domin kuwa tararuwarsa na haskawa, kuma yana da farin jinni a wajen yan kallo, gas hi mutum mai dadin hulda kamar yadda abokansa da na kusa suka tabbatar.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*