Ni Ban Zagi Atiku Ba Kuma Ban Goyi Bayan Buhari Ba, Inji Rahma Sadau

Jaruman Finafinai Hausa, Rahma Sadau ta karyata labarin da ya ta yawo a kwanakin baya na cewa ta zagi tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar dangane da martani da ya mayar wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan jawabisa a kasar Ingila.
Ta tabbayar da hakan ne a wani jawabi da jarumar ta aike wa jaridar Daily Trust a rubuce kamar yadda jaridar ta bayyana, jarumar ta kuma bayyana cewa ba ta goyi bayan shugaba Muhammadu Buhari a matsayin dan takaranta a xaben 2019 ba.
Rahma ta ce ta fito ne domin ta bayyana wa duniya gaskiyar jita-jitan da ya yi ta yawo a kafafen sadarwa wai ta zagi jam’iyar PDP tare da dan takarar shugaban kasa a jam’iyar.
Rahma Sadau ta kara da cewa tana alfahari da kasarta Nijeriya kuma duk da cewa kowa na da ‘yanci fitowa ya bayyana ra’ayinsa da kuma ‘yancin zabe, ta ce ba ta haka za ta fito ta bayyana ra’ayinta ba.
Daga karshe ta bayyana bacin ranta tare da kira ga jama’a da su yi watsi da duk wani labari makamancin hakan domin ba ita ba ce wasu ne kawai suke kokarin aran bakinta su ci mata albasa.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*