Kotu Ta Bada Belin Tsohan Gwamna Shema

…Bayan Kwashe Kwanaki Uku A Ma’ajiyar EFCC
Daga Jamilu Dabawa, Katsina
Kotun tarayya dake zamanta a Katsina, ta bada belin tsohan Gwamnan Katsina Ibrahim Shehu Shema, a karar da Hukumar EFCC ta Shigar a gabanta akan tuhumar zarge zarge ashirin da shidda kan karkatar da kudi har naira miliyan dubu biyar da dubu dari bakwai na asusun Hukumar Sure-P ta Katsina.
An bada belin sa bisa ga kimarsa na Tsohan Gwamna Katsina, kuma yana fuskantar shariar ta karkarta da kudin kananan hukumomi har naira Biliyan sha daya a gaban babbar Kotun jiha karkashin mai Sharia Maikata Bako, kuma ya bada shi belin.
Mai Sharia Babagana Ashgar ya umurce Tsohan Gwamna Shema da ya damka takardun tafiye tafiyensa wato (passport) a gaban Kotun. Alkali Ashgar ya dage cigaba da sauraren karar har zuwa 13/Yuni/2018.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*