EFCC Takama Wani Jigon Jam'iyyar APC Da Makudan Kudade

Hukumar yaki da rashawa, da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta sanar da kwato naira miliyan dari hudu da saba’in da uku, (473) daga cikin naira biliyan hudu da miliyan sittin da takwas (4.68bn) da ake tuhumar wani jigo a jam’iyyar APC, da kuma wani tsohon gwamna suka sata.
EFCC ta zargi tsohon ministan Jonathan, Musliu Obanikoro, wanda jigon ne a jam’iyyar APC da tsohon gwamnan jihar Osun, Iyiola Omisore da laifin raba naira biliyan 4.68 a gabanin zaben gwamnan jihar Osun, da nufin tafka magudi da aringizo a yayin zaben.
Daily Trust ta ruwaito hukumar EFCC ta samu nasarar kwato makudan kudaden daga hannun wadanda ake zargi a yayin da ta kammala shirye shiryen gurfanar da wadanda take tuhuma gaban kuliya manta sabo.
Majiyar Jaridar NAIJ ta ruwaito EFCC ta kwato naira miliyan 350 daga cikin naira biliyan 1.7 da gwamnatin Jonathan ta baiwa Omisore ta hannun Obanikoro don ya sake tsayawa takara a zaben gwamnan jihar Osun.
Yayin da hukumar ta kwato naira milyan 123 daga hannun Obanikoro, wanda yace tsohon mashawarcin Goodluck Jonathan kan sha’anin tsaro, Sambo Dasuki ne ya umarce shi ya kai ma Omisore kudaden, shi dan aike ne kawai, inji shi.
Binciken hukumar EFCC ya tabbatar da cewar Sambo Dasuki ya baiwa gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose zambar kudi naira biliyan 1.3, sa’annan ya kara masa dalan Amurka miliyan 5, duk don gudanar da yakin neman zaben gwamna a shekarar 2013.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*