Buhari Ne Zaizabi Mataimaki Ba Jam'iyya Ba

Jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba zata yi
kokarin kakabawa shugaba Buhari abokin
takara a zaben 2019 ba idan ya yi nasarar
samun tikitin takara.
Kazalika jam’iyyar ta APC ta ce ba zata
matsawa shugaba Buhari daukar
mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a
matsayin abokin takarar sa ba.
Sai dai a yayin da ya bayyana niyyar sa
ta sake tsayawa takara a ranar Litinin
da ta gabata, Buhari, bai ambaci da
waye zai sake yin takara a matsayin
mataimaki ba.
Buhari da Osinbajo
Kazalika bai nuna wata alama dake
nuna zai jingine mataimakinsa Farfesa
Yemi Osinbajo ba.
Sakataren yada labaran jam’iyyar APC,
Malam Bolaji Abdullahi, ya ce ba zasu yi
kokarin yin nune ko zabawa Buhari
mataimaki ba.
Wasu kusoshi a cikin jam’iyyar APC da
tun a shekarar 2015 basu so yadda
Tinubu ya yi uwa ya yi makarbiya a
batun tsayar da Osinbajo tare da Buhari
ba, na kokarin ganin a wannan karo
sun danne karfin Tinubu ta hayar canja
Osinbajo a matsayin abokin takarar
Buhari a zaben 2019.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*