Bazamu Sake Yarda Da Mulkin Talauci Ba – Tsofaffin Yan Bindiga Ga Buhari

Tsoffi masu fafutuka, karkashin kungiyar tsoffin yan bindiga, NAE ta nuna adawa ka kudirin shugaban kasa Muhammadu Buhari na sake takara a karo na biyu.
Kungiyar tace yan Najeriya bazasu sake yarda da wasu shekaru hudu na gwamnatin talauci ba.
Kungiyar wacce tayi ikirarin cewa tayiwa Buhari aiki a zaben 2015, tace ta janye goyon bayanta ga shugaban kasar.
Tace gwamnati mai cit a kawo tarin talauci, ta yasar da magoya bayanta sannan kuma tayi rashin adalci ga yankin Niger Delta.
A halin da ake ciki, Ciyaman na tarayya na jam’iyyar PDP Prince Uche Secondus yace jam’iyyar tasu bazata iya kada jam’iyyar adawa ta APC ba idan har basu hada kawunansu ba.
Secondus ya bayyana hakan ne a taron masu zartarwa na jam’iyyar ta PDP, inda yace sai sun hada kawunansu sannan zasu iya cire jam’iyyar adawa ta APC daga kan mulkin kasar nan.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*