Zamu Dakatar Da Shirin Mallakar Makamin Kare Dangi – Gwamnatin Koriya Ta Arewa

Matashin shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jun-Un ya tabbatar ma Duniya cewar kasarsa a shirye take ta yi watsi da shirinta na sarrafa makamin kare dangi, wato Nukiliya, matukar kasar Amurka da China zasu samar da yanayin zaman lafiya ingantacce.
Kim ya bayyana haka ne a wani ziyarar ba zata da ya kai zuwa kasar China a ranar Talata 27 ga watan Maris, ziyararsa ta farko zuwa wata kasar waje tun bayan darewarsa mukamin shugaban kasa, inji rahoton BBC Hausa.
Majiyar NAIJ ta ruwaito a yayin gawanar tasu, shugaban kasar China, Xi Jinping ya fada ma Kim cewa kasar China na nan kan matsayarta na raba yankunan Koriya da makaman Nukilya.
Wadannan maganganu da suka fito daga bakunan shuwagabannin biyu na alanta kyakkyawar zato da ake yin a cewar kasar Koriya ta Arewa zata yi watsi da shirin samar da Nukiliya ba tare da an kai ga baiwa hammata iska ba.A nasa bangaren, Christopher Hill, tsohon mai shiga tsakani akan shirin mallakar Nukiliya na Koriya ta Arewa, ya bayyana wannan ganawa tsakanin shuwagabannin biyu a matsayin abu mai muhimmanci.
“Gwamnatin kasar Sin ta nuna ma Kim cewar ba zasu yi maraba da shi ba, har sai ya koma turbar aniyar yin watsi da shirin mallakar makaman kare dangi, don haka a yanzu ana sa ran Kim zai bayyana ma shugaban kasar Amurka manufarsa ta yin watsi da makaman Nukili, a wata haduwa da ake sa ran zasu yi.” Inji Hill.
Source :naij hausa

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*