Connect with us

Gida Nijeriya

Arewa Ne Babbar Matsalar Nijeriya – Kungiyar Yarbawa

Published

on

Babban Sakataren kungiyar Dattawan Yarabawa, Dr Kunle Olajide, yace Arewa ce babbar matsalar da kuma cikas ga cigaban Najeriya.Olajide ya fadi hakan bayan jawabin da shugaban kungiyar Dattawan Arewa, Alhaji Ibrahim Comassie, yayi inda ya ke cewa Najeriya bazata rayuba idan ba Arewa.
Olajide yayi jawabi ne a Osogbo, ranar Alhamis, a wata lakca ta tinawa da Nathaniel Abimbola, wadda kunngiyar ‘Yan Jarida na Najeriya suka shirya a jihar Osun.
Olajide wanda shine ya shugabanci taron, yace ‘yan kungiyar Boko Haram sun yi kaka gida yankin Arewa, inda hakan ke janyowa gwamnatin tarayya asarar biliyoyin kudade, fadan addini, ‘yan ta’addan Makiyaya, da kuma matsaloli ga cigaban rayuwa.
Wani Mamba na majalisar wakilai na jihar Osun, Prof. Mojeeb Alabi, shima yayi jawabi, yace rashawa ba ita bace asalin matsalar Najeriya ba, amma dokar kasar ce keda matsala. Ya kara da cewa rashawa itace makasudin matsalolin da ake samu dokar kasa wanda hakan ke janyo zargi a gun al’ummar kasa.
Source :naij hausa

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Facebook

Advertisement

Trending