NI DA PRINCE PART 5

By  *[truncated by WhatsApp]
[11/13, 10:47] πŸ’žMaman BinafahπŸ’ž: β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„
πŸ’₯ *NI DA PRINCE*πŸ’₯
β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„

*NA AYUSHER MOHD*

NO.5⃣2⃣

An gama karama Salma jini Salman ya mike da kyar dan jiri yakeji, kusa da ita ya zauna tare da riko hannunta, zeena kam jikinta yai sanyi, tana mamakin tsananin san da Salman kema Salma.

Salman na zaune har barci yafara d’aukansa hakan yasa ya kwantar dakansa kusa da ita, ahankali bacci yai gaba dashi, Salma sai datakai wajen karfe 3, alokacinma mafarki take, wai Salman sunyi fad’a ya juya zai tafi tabishi da gudu tana kira, sai dai kafin ta karaso ya b’ace mata, a firgice ta mike tace *PRINCE*cikin wata murya, dukansu sai da suka tashi zeena, Salman ya kankame hannunta yace” Naam beauty ganinan.”

 Bata kula da kowa ba kawai rungumeshi tau kam tana hawaye, shima hawayen ne ya zubomai, a hankali ya nemi ya d’agota amma ina….kara k’ankameshi tai, Salman yai ajiyar zuciya yashiga shafa bayanta.
 Zeena kam tayi mutuwar zaune tana mamaki itakam bata tab’a ganin masu san juna irin haka ba.

 Salma ta dade ajikin Salman kafin ta d’ago, ahankalita tab’a fuskarshi,sai alokacin abinda yafaru ya dawo mata, a hankali tace “ba abinda ya sameka? Salman ya shafa kanta yace “ba abinda yasameni sai tsoron abinda yasami matata.”

 Salma ta share kwalla, tare da tab’a kanta datajishi a d’aure, jin plaster yasa ta d’aure tace “na d’auka zan rasaka.”

 Salman yai shiru, ishaq ne ya fad’o mai arai, sai kuma ya share, tare da kamo hannunta yace abinci fa? Tace zanci, mikewa yai sai alokacin yaga zeena, ya sosa keya, itama Salma sai alokacin ta ganta, dasauri ta koma ta kwanta, ta rufe fuska, zeena tace ” a’a love birds bansan wani salo, angama fitsara agabana sai kuma ashiga rufe ido?”
 Salman yace “kema yaya zeena da kika ga haka sai ki koma ki kwanta.”
 Tace “au to ayi hakuri na koma bacci.”
Tafad’a tare da kwanciya.

 Dakanshi ya zubo mata abinci ya sa spoon ya matso kusa da ita, Salma ta mike a hankali tare da kallan agoggo, ta kalli Salman tace “wai ukun darene tai?”
 Salman yace “eh mana duk kin gama tsoratani, ganin baki farka ba.”

 Tace ” Yahkuri.”
 Yace “ci abinci dai tukunna.”
Da kanshi ya shiga bata, tayi spoon biyu ta kalleshi tace” kaima nasan bakaci komai ba, sai dai muci tare.”
 Zaiyi magana tace “please”
Yai murmushi yace ok.
Tare sukaci, sai da suka koshi sannan ya bata ruwa tasha, ta kalleshi tace “prince mud’anfita?” Kai ya d’aga mata tare da taimaka mata ta mike.
Suna bude kofa yaga fadawa da sauri ta koma tace mun fasa, Salman ya kalleta yace “meyasa”
Komawa ciki tai tare da zama a kan carpet d’in dakin, Salman ya d’auko bargon dake kan gadon ya karaso kusa da ita ya zauna tare da rufa musu bargon, Salma ta kwanto da kanta kafad’arsa tare da zura hannunta jikin hannunsa.

 Salman ya sa d’ayan hannunsa kan cikinta yace “babyna dafatan kana cikin koshin lafiya.”
 Salma ta kalleshi da mamaki tace ” baby?, wa kenan, badai suna aka canzamin ba?”

 Salman yai murmushi yace “babyna mana dake jikinki, wai ya akai baki sani ba?”
Salma ta d’aga kanta daga kansa tace” naam?” Salman ya d’aga mata gira, tace “muga wayarka?”

 Nan Salman ya mika mata ta amsa tare da duba date, Dagaske ta wuce kwanankin period d’inta da 9 days, amma ya akai bata sani ba? Kallan Salman tai cikin farin ciki tare da shafa cikinta, ko shiyasa kwananan sai tai tajin kwad’ayi?.

 Salman ya maido da kanta inda yake tare da cewa Beauty kiyi Sauri ki warke mu kula da babynmu, Salma ta d’ago da d’an karfi, jin kanta yad’an amsa tace ahhh.
Salman da sauri ya kalleta yace “beauty?menene? Zafi?”
 Salma tai murmushi tace kan nawa ne sai injishi a d’ad’aure bansaba ba yace ” haka ne ai, sannu, amma beauty da kika ture ni aka bige ki kinsan me kikai kuwa? Kina tunanin zanso wani abu ya sameki akaina?”
Salma ta maida kanta tace ” ni alokacin gaba d’aya kaina ya kulle tsoro na d’aya kar wani abu ya sameka.” Kwalla ta cika idanta tace ” namanta da jikina, ni kawai kai nake gani.”

 Salman yai shiru, tare da lumshe ido, Salma jin haka tace “kasan mafarkin danai? “
Salman yad’ago ya kalleta, tace bazan fad’ama ba siri ne.
Yai murmushi yace in ansan siri ne ai ba sai an min zancen ba dan a samin san jin labarin.
Salma ta kara gyara kanta tare da rufe idanta, Salman shima ya rufe nasa idan, bacci ne ya d’aukeshi, a hankali Salma ta mike tare da wucewa toilet tai alwala, Sallah tazo ta tada ta rama salolin da ake binta.

Da safe zeena dakanta taje gun likita tace ya kamata a sallamesu dan da akama bazasu iya zaman asibiti ba, likitan yace to amma sai zuwa yanma tace to, sannan ta koma ta sanar musu.
Salman kam ba kunya dadi yaji.
Wajen karfe 9, Farha ta taho damai kawo abinci, tsoron shiga takeyi hakan yasa tace masu kaiwar su shiga dashi, ita kuma ta tsaya ajikin window tana kallan Salman dake zaune kusa da Salma, wani abu ta had’iya idanunta suka kad’a, kamar wasa Salman ya kalli window, Farha ya gani tayi tsuru, murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan tazo, Salma ta kalleshi tare da had’e rai, Salman yai kamar bai ganta ba.
 Farha na shigowa jiki a sanyaye ta d’an tsaya daga nesa yace “kanwata matso mana.”
Farha ta d’ago ta kalleshi cikin mamaki, Salma ma kallan mamaki take mai, Farha ta matso kusa tare da gaidashi ya amsa fuska a sake yace” meye na tsayawa acan.” Tace “uhm yaya dama ai…”

 Ya katseta yace ” inkinzo neman lada ki nema da kyau” ahankali tace to.
Sannan ta kalli Salma dake kallanta rai a b’ace tace “in_law sannu da jiki”
Salma tace “yauwa”fuska a d’aure, farha tad’an dade kad’an kafin tace “bari in tafi yayana.” Salman ya kalleta yace “to Farha nagode” murmushi tai tace “nice da godiya yayana.”
Nan ta juya tai waje, Salma ta bita da harara tace “daka bita ai” Salman yace “ko?to in na batta ke kuma fa?.”
Haushi ya kamata tace “ai bakaikad’ai bane a guna.”
Ga mamakinta gani tai Salman ya mike, yai waje, ta kalleshi cikin tsananin mamaki, menene hakan?

 Salman kam yana fita ya had’e rai tare da bin inda Farha tai, tana tsaye a jikin wata bishiya, tana waya, a hankali ya karasa inda take, jiyai a wayar tace “wlh yaya bai nunamin komai ba” bai ji me akaceba yadaiji tace ” yama za’ayi ace Salma keda ciki bayan ni ya kamata infara haifar mai d’a? Fulani Nifa na tsani Salmar nan, kyau kamar aljanna.”
Salman ya kalleta cikin tsananin b’acin rai, ga mamakina sai gani nai ya dawo ta gabanta da murmushi yace na fito miki rakiya ashe kina nan? Tsoro ya kamata ta kalleshi tare da yarda wayarta, Salman yace “ahhh Clumsy girl, yazaki yarda wayarki?”
Dasauri tad’auka tare da kashe wayar.
Salman yace “da alama rakiyar bazata yiwuba bari na koma gun beauty.”
Farha da sauri tace “a’a inaso yayana”
Salman yai wani murmushi yace “muje to, ina kikai parking?”
A hankali ta nuna mai inda motarta take, dakanshi ya rakata sai daya tsaya ta ja tai gaba, sannan  yabi motar da kallo yace ” one by one ni zan koya muku hankali.”
Farha kam farin ciki tad’inga jin jitake kamar tai ihu dan dadi.

Salma kam ta cika tai fam……..
Nace to fa!!! Kowa da abinda ke ransa….lol

By *Ayusher Mohd*πŸ“š
Β© *NWA*
[11/13, 10:47] πŸ’žMaman BinafahπŸ’ž: β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„
πŸ’₯ *NI DA PRINCE*πŸ’₯
β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„

*NA AYUSHER MOHD*

*This Page Is Dedicated To My Besty DizzyHrt😍😘*

No. 5⃣3⃣

 Salman ya koma d’akin inda ya tadda Salma a kwance, Zeena ya kalla yace bacci tai? Yafad’a tare da kallan Salma, Zeena “tace Na fito daga wanka naganta akwance maybe  baccine ya d’auketa.”
Salman ya zauna a kusa da ita tare da kallanta, idanunta a rufe suke tanaji zeena tace bari taje waje zatai waya.
Salman na gani ta fita ya matso daf da ita tare da sako fuskarshi daf da tata, yakai bakinshi gefen kunnenta yace “beauty nasan fa ba bacci kike ba”
Salma ta shareshi, bakinsa yakai inda akasa mata plaster ya sumbata, salma a hankali ta bud’e idanunta, ta kalleshi.

 Salman ya d’ago idanunsa suka had’a ido, tace “har ka dawo?” Yace “Beauty ba inda ke miki ciwo dai ko?” Salma ta kalleshi har zatai magana ta fasa, can tace ” ka fad’ama su Abba ne?” Salman yace ” tun jiya nakesan sanar musu amma ina tsoron kar hankalinsu ya tashi.” Tace “gwara da baka fad’aba dama banaso susani, hankali Abba tashi zaiyi.”

Da yamma hajiya karama da kanta tazo ta taho dasu Salman, ba shiri suke ba hakan yasa daga gaisuwa da dubasu ba abinda yakara had’asu har suka isa.

Salman suna shiga ya kalli Salma yace “ina zuwa dear,” Salma tace to.

Bangaren Fulani ya nufa, yana shiga ya wuce kilisarta, tana zaune itada Ishaq abin duniya ya damesu, jin sallamar Salman yasa suka kara shan jinin jikinsu, Salman ya shiga tare da neman guri ya zauna.
Cikin murmushinsa dabazaka tab’a gane me yake nufi ba yace” Umma tunda ke kin kasa zuwa dubo d’anki shi gashi yazo da kansa.”

 Fulani ta shiga in in na tace ” Salman ba haka bane yanzu nake shirin fita, amma nikam ya akai hakan tafaru?” Tafad’a dan tabbatar da Salman yaga Ishaq
Salman ya kalleta yace ” Hmmm to Nikaina bazance ga abinda yafaru ba, amma nikam kamar kana gun ko?” Yafad’a tare da nuna Ishaq, kan kace me? Ishaq ya rikice, jikinshi yafara rawa.
Salman yai wani murmushi yace ” to ko ba kaina gani ba? Sai naga kamar kai ka taimakemu ka kaimu asibiti?”

Fulani jin haka yasa tai saurin cewa ” shine mana, kasan halin Ishaq da rud’ewa, ya firgita ne ganin halin da kuka shiga.”

 Salman yace ” ohhhh naga alama, nikam ina Farha?”
Fulani tace “tana d’akinta, hankalinta ya tashi dataji halin da kake ciki”

 Salman yace “nasani ai.” Yafad’a tare da mikewa, har yakai kofa yaji Fulani tace “Amma naji kamar ance kanada wani ciwo? Mai wuyar warkewa?”
 Salman ya tsaya cak, tare da cizen leb’e, ya juyo inda suke ya saki murmushi yace ” ba wani ciwo, kawai ganin matata tashiga wani yanayi ne yasa nima na shiga, ya akai? Kin shiga wani haline jin banida lafiya?”
Fulani tad’an tab’e baki tace “sosai ma, Alhamdulila da abun ba serious bane.”
Salman ya juya batare daya mata magana ba.

D’akin farha ya isa tare da knocking,  ta budemai, sai dai ganin Salman ya sa ta saki baki, Salman ya karasa d’akin yana cewa “to ko ba’ayi farin cikin ganina bane?”
Farha ta juya ciki da sauri tace “yayana, kaine?”
Yace “me? Bakiyi farin cikin ganina bane?”
Tace “inafa!!! Farin ciki yaimun yawa dai.”

    Salman ya karasa jikin madubi inda take yaga takardu, ya d’aga tare da cewa “badai anan kike ajiye passport d’inki ba?”
Farha tace a’a  takarasa cikin jakarta tare da cirowa tace “ka ganshi nan”

 Salman ya karasa ya ansa yace ” banyarda adinga ajiyeshi a jaka ba, dan haka nizan ajiye miki daga yau.”
Farha ta rufe ido tace ” jinake kamar ka zama mijina yayana”
Salman ya buga mata wani kallo sannan ya karaso daf da ita, yace “lokacine ai.”

 Farha kam kamewa tai a tsaye har Salman ya fita bata sani ba, Salman na fita ya d’aga wayarsa ya kira wani friend d’insa, yace ” zan kawo maka passport d’in gobe, please as soon as possible nakeso.”

 Ya kashe wayar tare da sakin wani murmushi,  yace bazan bari ki kara canza hali ba anan garin.

 Salma kam d’akinsu ta shiga gyarawa, Salman ya bud’e kofar, tana tsaye jikin gado ta juyo ta kalleshi,  Salman ya karaso tare da bud’e mata hannu, murmushi tai, takaraso ta shige jikinsa, riketa yai tsam yace beauty kamar munyi wata bama d’akin ko? Tad’aga kai, yace “ahhh naji dad’in ganin mu, mu biyu, Salman ta kara shigewa jikinsa, rikota yai ya zaunar da ita kan gado, tare da mikarmata da kafarta, yace “ki d’inga zama kina hutawa sosai, karki d’inga wahalarmin da babyna.”

 Salma ta rangwad’ar da kai tace “Prince gyaran d’akin ma wahala ne?” Yace “eh mana.”
Tace ” to ai sai jikina yai tsami in haka ne.”
Mikewa yai ya zauna a bayanta sannan ya kwanto ta jikinsa, yace “Beauty?” Tace “naam.”

 Yace ” nikad’ai nasan farin cikin danake ciki.”
Tace “ummm to in haka ne abani gift”
Yace “toh!! me Beauty na takeso?”
Ta juya kanta tace ” exams dazakuyi this year, karka m’ika farar takarda.”

 Salman ya sakar mata murmushi yace “daga sanda naji kina da ciki, na d’au wannan alkwarin, bazan bari d’ana yataso yaganni coward ba.”

 Salma ta kai bakinta zata sumbaci kuncinsa, matsowa yai hakan yasa bakinta ya shiga nashi, tad’an d’ago ta kalleshi, hannu yasa a gefen fuskarta yakara jawota kad’an, shima ya matso,  tare dakai bakinshi cikin nata, sun shagala sosai, salo suke ma juna, dukansu idanunsu a rufe, sun dade kafin su saki juna, a hankali Suka bud’e idanunsu, Salman ya had’a gushinsa danata, suka saki murmushi,  tace thanks dear………murmushi ya sake mata.

A ranta tace Allah nagode maka daka had’ani da wannan bawa naka.

Farha kam tsalle ta daka, jitake kamar ranar auransu ta zo, waya ta d’aga takira mumynta, tace “mumy bana tunanin zan dawo yanzu, maybe ma kune zaku taho, bani ba.”
Mumyn tace ” bangane ba”
Farha tace ” kedai bari mumy, burina ya kusa cika.”tafad’a tare da kashe wayar, tace “hmm wayaga idanun Salma?”

 Lol…..nace har na hango….

By *Ayusher Mohd*
[11/13, 10:47] πŸ’žMaman BinafahπŸ’ž: β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„
πŸ’₯ *NI DA PRINCE*πŸ’₯
β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„

*NA AYUSHER MOHD*

No.5⃣4⃣

Salman yashirya tsaf, Salma dakanta ta d’aukomai kaya ya saka, suka fito dinning Salma ta zauna ta zubamai abinci, Salman ya kalleta yace “yauma nikad’ai zanci?” Tace “a’a tarw zamuci” yai murmushi tare da kallan su hanne, ya musu alama da hannu su fita, nan sukai baya suka fita.
Salma ta sa spoon suka faracin abincin, Salman sai kallanta yake yana murmushi,  suna gamawa ta d’auko mai littafinshi da mik’amai, yace “thanks dear” tace “Allah ya bada sa’a.”
Salman ya mata kiss a kumatu sannan yai waje.
Direct school ya wuce, a hanya yama Najib waya yace “nashigo, ka karaso?” Najib yace ” yanzu na shigo kana ina? Naji kace akwai magana.”

 Salman yace mu had’u a inda muka saba zama, ya kashe wayae tare da karasawa.

 Sun had’u su uku da Amir, Salman ya kallesu sannan ya kalli agoggo yace “saura 5mins a shiga lectures, let me go straight to the point,  daga yanzu no more play.”
Najib da Amir suka kalleshi da mamaki, sukace yarima me kake nufi? Salman ya d’aga littafin hannunsa yace ” Nadaina submitting d’in blank sheet, na kusa zama uba, ba zan bari d’ana ya taso yaganni a haka ba.” Yana kainan yai cikin theater,  suka bishi da kallo cikin tsananin mamaki, anya Salman ne kuwa? Sai dai Najib ya kalli Amir yace ” kamar cewa yai ya kusa zama uba ko?”
Amir yace “haka naji.”
Najib yai murmushi yace “wow da alama Salma ciki gareta.”
Shima yai sauri ya shiga yana murna.
Amir ya bisu da kallo, shikam sam baisan karatu, haka dai ya shiga ranshi a b’ace.

Yan class gaba d’ayansu suka zuboma Salman ido, harda malamin, mamaki suke yau Salman ne ya shigo akan lokaci? Sannan kuma rike da littafi? Salman ko kulasu baiyi ba ya wuce ya zauna.

  Malamin ya saki baki, sai da Salman ya kulu yad’an daki desk kad’an, sannan kowa ya juya,  malamin ya d’auko biro a aljihunsa a rikice ya d’auka maker ce, sai dayaje rubutu ya gani, yan class suka kwashe da dariya, sannan yai saurin d’auko maker ya fara rubutu.
 Salman rashin sabo yasa duk yaji ajin ya isheshi, yadaure sai gyara zama yake, yakai hannu kamar zai d’auko waya, Najib yace “ka manta ne baban baby?” Salman najin haka ya fito da hannunshi, har aka gama lectures kafin su fito.

Yana fitowa yad’au wayarsa ya kunna, text ne ya shigo daga Beauty “My prince ya karatun?”
Murmushi Salman yai sai dai maimakon ya kirata kawai sai ya kira wata number,  yace “Asim ina zamu had’u? Na taho da passport d’in.”
Sai kuma yace “alright” tare da kashe wayar.

 Najib ya kalleshi yace “badai honeymoon zaku kara guduwa ba?” Salman yace to baban sa ido, mun kusa fara exam inafa zani wani gun?” Najib yace “kai abin nan na bani mamaki.”
Salman ya d’an bige kafad’arsa yace ” gwara ya daina ma baka, muje ka rakani.”

 Nan suka shiga mota suka fita.

Farha zaune kusa da fulani da ishaq, Fulani tace “yanzu wace shawarar zamu b’ulo?” Farha ta kallesu tace “ni ba wani plan da za’ayi dani, dan yanzu yayana yana sona banason nasake wani abu dazaisa ya kara jin haushina.”
 Fulani tace ” ke yanzu kina tunanin Salman dagaske sanki yake.”
Farha ta mike tace” ni ba abinda yadamen, abinda yayana Yafad’a dashi kad’ai zan d’inga amfani.” Takarashe maganarta tare da mikewa tai d’akinta.
Ishaq yace “good haka akesan soyayya da confidence,  da alama nima zan tari Salma in fad’a mata abinda ke raina, wayasani ko itama tana sona? Ganin na basar ne yasa ta share?”
Fulani ta kalleshi shekeke, tace “lalai Ishaq baka da hankali, matar kanin taka zakace kana so? “
 Ishaq ya mike yace “nidai nagaji da biye miki abubuwa na basa tafiya daidai.”shima ya juya yai waje.
Tai tsaki tace “ace duk cikinsu bada wanda zakai shawara? Ga ragowar ‘yayanta maza bata saba irin wannan had’in dasu ba.

Salman sai bayan magrib ya dawo, yana parking yaga wayar farha,  tsaki yad’anyi kafin ya d’aga, cikin salo da kisisina take maganar, tace “yayana baka dawo ba?” Salman yace “ya akai? Kanwata ta damu ta ganni ne?” Farha tace “sosai ma.” Yace na shigo yanzu, anma zan tsaya gun mai martaba”
Tace ” to sai ka gama.” Ya kashe wayar batare da ya amsa ba.
Tsaki yakari yi, sannan ya kira Beauty, Salma ta d’aga tare dayin sallama, wani sanyine ya ratsashi, yace Beauty kinjini shiru ko? Tai murmushi tace ” eh mana duk ba dadi.” Salman yace “uhmmm lalai an damu dani dayawa, Me aka tanadarmin to?” Salma tace “komai ma, nidai ka dawo please”

  Salman yace ” amma dai ba inda ke miki ciwo ko?” Tace “nurse tazo d’azu ta dubani tamin dressing.” Yace “good, na iso ma, zan d’an shiga gun mai martaba ne” tace “tam a mikamin gaisuwata.” Yace “uhmm.”

 Ya kashe wayar tare da fitowa yai b’angaren mai martaba, yana isa, bafadan ya shiga yamai iso, Ishaq na zaune gun sarki, Sarki ya bada izini.

 Salman na shigowa yaga Ishaq,  shima Ishaq din kallanshi yake, Salman ya d’auke kai, tare da shiga,  yai kasa dakai sannan ya kwashi gaisuwa, ga mamakin Ishaq bayan  Sarki ya amsa harda tambayar jikin Salma, cike da mamaki Ishaq ya kalli Sarki, bai kara shan jinin jikinsa ba sai dayaji Sarki yace Ishaq bamu guri zamuyi magana, cikin tsananin mamaki ya amsa sannan yafita, sai kuma yai tunani ko dai fad’a za’amai? to amma in fad’ane ai sarki bazai amsa gaisuwarsa ba, meke faruwa?.

Nace kaika sani…………

Salman ya dade sosai, da  Sarki sai daya tirkeshi suka ci abinci tare, sannan yamai saida safe ya fito.

Kana ganin fuskarsa zaka gane yana cikin farin ciki, yau ce rana ta farko daya tab’a cin abinci da mahaifinsa, bazai iya tunawa ba ko kila yana yaro, amma shidai a saninsa yau ce ranar farko.

Bangarensa ya shiga da sauri, shi sam bai kula da Farha dake zaune a falo ba, zuciyarshi nakan yasanar ma Beauty abin farin cikin daya same shi, Salma kam, tayi kwalliya da riga iya gwiwa, da d’an wando pencil, ya d’ameta, ta fito daga toilet kenan, jin kamar zatai amai, sai dai taje ta kuma kasa aman, jitai an murd’a kofa ta juya dan tasan Salman ne, ganinshi tai ya shigo da sauri, yana shigowa ya sa hannu ya d’agata yafara juyi da ita,  Salma tace “Prince? Wani abun ne yafaru?”
Sauketa yai sannan ya rungumeta yace “Beauty kinsan me?” Ta girgiza kai alamar a’a, yace “yau tare mukaci abinci da Abbana.”

Wani sanyayen farinciki ne ya bayyana a fuskarta tace” Prince?  Naji dadi sosai”
Shima yace “nima haka beauty.”

Farha da kishi ya turnuketa ganin Salman ya wuceta yasa tabuga kofar da karfinta, Salma da Salman suka kalli juna, Salma ta karasa tare da bud’e kofar ta fita.

Farha ta gani hakimce akan kujera, tace ” Yayana nake nema” Salma tace “haka b’atan kai kikai ko? Kin manta na hanaki shigomin guri?”

 Farha ta d’aga waya ta iira Salman,  ya d’aga tace “yayana ina falo fa?” Tai maganar cikin shagwab’a, Salma tai wani murmushi tace wahalace bata isheki………maganarce ta tsaya a wuya ganin Salman ya fito, cikin mamaki tace “Prince?” Salman ya kalleta sannan ya kalli Farha yace “kinzo?” Ta makama Salma harara sannan tace “tun d’azu nazo fa, ina nan ka wuceni.”

  Salman ya kalli Salma data cika tai fam, ya kalli Farha yace “muje waje.” Tace ” to” sannan ta kalli Salma tace “inlaw Sai da safe.”
Salma ai kasa magana ma tayi tana kallansu suka fita, bin kofar tai da kallo…….

Mekenan? Abinda ke yawo akanta kenan.

By *Ayusher Mohd*πŸ“š
Β© *NWA*
[11/13, 10:47] πŸ’žMaman BinafahπŸ’ž: β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„
πŸ’₯ *NI DA PRINCE*πŸ’₯
β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„β˜„

*NA AYUSHER MOHD*

No.5⃣5⃣

Salman suna fita ya kalli Farha yace ” gani neman me akemin?” Ta saki wani murmushin kissa cikin shagwaba tace ” nemanka kawai nake in ganka, jinake kamar na dade bam ganka ba.”
Wani kallo ya mata da ita kanta batasan nameye ba yace ” idan bakya garin yazakiyi kenan?” Cikin rashin fahimta tace ” bangane ba yayana.” Salman yai murmushi shima tare da matsowa kad’an yace “just joking. “
Dariya tasa tace ” kai yaya har ka tsoratani.” Yace ” yanzu dai nagaji, muje in rakaki in dawo inkwanta, bacci nakeji.”
Cikin salon shagwaba tace ” ba wani yaya so kake dai ka koma gun matarka.” Gani tai ya murtuke fuska ya had’e rai sosai yace” in muna magana karki kuskura ki kara sako matata, banasan haka.” Farha kam jitai jikinta yai sanyi, a hankali tace “kayi hakuri yayana.”
Murmushi taga kuma ya mata, yace “ba haushi naji ba kawai banaso ne.”
Tace “to yaya, zan kiyaye.”

Nan suka fita ya rakata sai dai bai shiga b’angaren fulani ba yace mata ” nizan wuce, sai na ganki gobe.” Tace ” to yayana. “

Salman ya juya ya taho, itakam tana tsaye tana kallanshi har ya kule, kafin ta shiga gida, waya ta d’aga ta kira mumynta, yanda taji muryar mumyn da alama bacci take ma.
Farha tace “Mumy natasheki ko?” Mumyn tace “ya akaine Farha?” Farha tace cikin rawar murya ” Mumy ina tsoro fa?” Tace “tsoron kuma me? Kamar ba ‘yata ba? Bansanki da haka ba.”
Farha tace ” ina tsoron in na auri yaya Salman da kyar insamu soyayyarsa ko wata kulawarsa.” Mumyn tace ” baya sanki ne?”
Farha ta share kwalla tace” Na kasa gane wa Mumy”
Mumyn tace ” indai kinasan abu na dade ina fad’a miki ki tabbatar abin nan yazama naki, rayuwa d’aya ce ba biyu ba, kar kizo kiyi dana sanin abun.”

 Farha tace ” ai abun nan danakeso Mumy dole ne ya zama nawa, ko me mutane zasuce.” Mumyn tace “good, ke dama har kina wani tunanin soyayya? Bayan nasan kinsan komai, a yanda nasanki, ina tunanin ba namijin da bazaki iya karkato dakansa ba, amma kike shirin bani kunya?”
   Farha ta zauna akan gado tace ” mantawa nai mumy, gashi Salman d’in kwarjini gareshi, ina shirya a d’aki zanyi abu, ina fita sai in kasa.”
Mumyn tace “to ko kinaso in ma yaya magana? Nasan dai zai duba maganata duk da ba uwa d’aya muke ba, inya duba hallarcin rike mai Salman danai, bazai ki ba” Farha tace ” haba mumy ni banaso inje gidan wannan ‘yar iskar matar tasa tad’ingamin wani kallo, nafisan in aureshi ta soyayya.” Mumyn tace shikenan sai naji good news tafad’a tare da kashe wayar.

Farha tabi wayar da kallo tace ” shiyasa nakesanki Mumyna.”

Salman kam yana shiga gida Salma ya gani tsaye a inda ya barta, baice mata komai ba kawai hannunta ya kama yai cikin d’aki da ita, suna shiga ya jawota jikinsa yace “Beauty me yasa zaki tsaya a falo bayan kinsan ba lafiya gareki ba.”
Salma ta daure tace ” ina kaje?” Salman yace ” Beauty do you trust me? ” tai shiru can d’aga kanta, Salman yace ” in har kin yarda dani then please just trust me.” Salma ta d’ago ta kalleshi idanunta taf kwalla, tace ” I trust you Prince but I don’t trust that girl.” Salman ya shafo gefen fuskarta sannan ya tsaida hannunsa akan gefen fuskarta, ahankali ta d’ago ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla, yace ” just trust me, kinji?” D’aga kai tayi alamar eh, nan ya kai bakinshi cikin nata, salon dasuke ma juna yasa suka gangara kan gado, sun shagala sosai da farantama juna rai, hakan yasa nikuma nai waje.

Da safe wajen 10 Salman bayan ya shirya yace itama ta shirya ya ajiyeta a gida, murna agun Salma kamar me, itakanta tanasan zuwa, tana tsakiyar murnarta sai kuna tai kasa da kai, Salman yace ya akai kuma? Ta nunamai inda aka mata d’inki  tace ” a haka zani?” Salman yace “zasu gani ko?”
Salma tace ” banaso su zargi komai, inciwon ya warke na kirasu a waya.”
Salman zaiyi magana wayarsa tai k’ara ya d’aga da sauri ganin Asim ne, yad’aga yace “abokina ya?”
Asim ya sanar masa yayi ciko ciko dan haka karfe 5 akwai flight dazai tashi, yai murmushi tare dayin godiya ya kashe wayar.

Salma ta kalleshi tace “wani abu ne?” Yace “is a secret bari inje gun mai martaba in dawo” tace to.
Dasauri ya fita, yai fadar mai martaba, akamai iso ya shiga,  sun gaisa cikin sakin fuska kafin Salman yace yanada magana, jin haka yasa Sarki ya bada umarnin abasu guri.

Salman ya d’an matso kusa da Sarki, yace ” Abba akan Farha ne.” Sarki yace “nikaina inasan inma magana akanta.”Salman yace ” name?”
Sarki yai shiru can yace ” d’azu da safe mahaifinta ya kirani akan wai Farha na sanka, kuma wai saboda kai tazo nan kasar.”
Salman ya had’e rai yace” wannan zancensu ne, ni yanzu tunani nake yau zansa a maida ita kasarsu, dan nakula zamanta anan nema yake ya canza mata hali daga good zuwa bad.”
Sarki yai shiru can yace ” bangane canza hali ba? ” Salman yace ” wasu suna amfani da ita akaina, nikuma nasan ta duk da she is not kind amma she is not bad.” Sarki yace ” su waye wad’anan mutanen?” Salman yai kasa dakai yace ” Abba abar maganar kawai.” Sarki yace ” shikenan amma da alama kenan baka san auran?” Salman yace ” Abba yarinyarnan kanwata ce, kuma koba haka bama ni bani da tsarin auren nace biyu. “
Sarki yai murmushi yace ” da alama d’ana yanzu yana fad’amin abinda ke ransa, naji dadi sosai, amma yanzu yazamuyi da iyayenta?” Salman yai wani murmushi yace ” ba wani abun bane ni zan fad’a musu” Sarki yace “good inasan confidence d’innan naka.”
Salman yai kasa dakai tare da sosa keya.

Kafin sallar la’asar Salman ya dawo gida, bangaren Fulani yai, tana zaune a kilisarta itada Ishaq, kallansu kawai yai yace Umma ina gaisuwa, Fulani haushi ya kamata, gashi agaban bayinta wannan ai cin fuska ne, Salman d’akin Farha ya wuce tare da knocking,  ta bude da sauri dan yasanar da ita zuwanza, a kofa ya tsaya yace ” Farha hado kayanki mu fita.”  Tace  ” kayana kuma yaya?”  Salman yace “eh wani gida zan kaiki.” Cikin rashin fahimta tace ina? Salman ya had’e rai yace ” in bakyaso mu barshi kawai, nad’auka zakifijin d’ad’in can da nan.”
Farha ta riko hannunshi tace  “ya hakuri yayana, bari na had’o”
Salman ya jingina da kofa yana jiranta, Ishaq ne ya taho a zuciye, yace ” kai Salman wato dan rashin mutunci, umma kama haka?”

Salman ya juya fuska sannan ya kara juyowa da murmushi yace “ahhhhh, dan nace ina gaisuwa?” Yafad’a tare da takawo zuwa gun umma, ya zauna sannan yai murmushi yace ” Umma ashe wai haushi kika ji?” Itama ta kakaro yake tace “haba Salman wani haushi kuma?”

Salman ya mike tare da kallan Ishaq yace “kaji ko? Dama yama za’ai taji haushi akan wannan? Intaji haushi ai da matsala.” Ishaq ya kulo yace ” kaifa d’an rainin wayau ne.”
Salman ya dafa kafad’arsa ya matso daf da kunnensa yace “rainin wayau ya wuce wanda kamin? Ka d’auka ban sani ba?” Yasaki wani murmushi ya wuce d’akin Farha.
Jikim Ishaq ne ya shiga rawa, badai ya sani ba? Me ya ke nufi da kalamansa? Bai fito yace yaganshi ba? To me yake nufi?
wad’annan tambayoyin su suka sa jikinsa ya shiga rawa.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Leave a Reply

Your email address will not be published.


*