Sarkin Kano Ya Dauki Nauyin Jinyar Mahaddacin Kur'ani Da Za A Yi Wa Dashen Koda

… Sarkin ya biya milyan shida domin yi wa mara lafiyan aiki
Daga Sa’adatu Baba Ahmad
Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, ya dauki nauyin mahaddacin alkur’anin nan da aka ce zai a yi wa dashen koda.
A kwanaki biyu da suka shude na ga Real Fauziyya D. Sulaiman ta yi posting neman taimako tare da halin ha’ula’in  da wannan bawan Allah ke ciki, Allah cikin ikonsa na mika wannan sako wajen mai martaba.
Ya ce zan je da kaina na duba shi kuma inshaa Allah zan biya naira miliyan 6 da Aminu Kano suka bukata domin ba zamu bar mahaddacin alkur’ani a cikin halin ko in kula ba.
Tun safiyar wannan rana mai martaba ya tura asibitin Aminu Kano da Nassarawa inda marar lafiyar yake aka shirya komi don ci  gaba  da kula da lafiyarsa.
Da yammacin yau kuma ya yi tattaki da kansa zuwa duba marar lafiya ya yi masa addu’ar samun lafiya tare da fatan Allah ya tashi kafadunsa.
Abinda ya fi ban tausayi marar lafiyar nan ya dauki alkur’aninsa ya dankawa mai martaba Sarki yace wannan ne abinda nake da shi kuma na baka. Allah ya sakawa sarki da alheri,  Naif Isma’il kuma Allah ya ba shi lafiya.
Daga Rariya

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*