Photos: Mata Sama Dubu Hudu Ne Suka Canza Sheka Daga PDP Zuwa APC A Jihar Katsina

Sama da Mata Dubu Hudu ne suka sauya sheka daga Jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyya mai mulki ta APC a yankin karamar hukumar Funtuwa ta Jihar Katsina, inda aka shirya gagarumar liyafa domin tarbar su karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari , wanda taron ya gudana a harabar gidan abinci na El Bintu Restaurant dake garin Funtuwa Jihar Katsina.
Lokacin da take jawabi a yayin taron, Hajiya Zainab Abdullahi Ghana wacce itace tayi jagorar karbar Matan daga PDP zuwa APC, ta bayyana cewar sauya sheka da wadannan dubban Mata sukayi zuwa APC, alama ce babba dake nuna nasarar Gwamnan Jihar Malam Aminu Bello Masari ta wajen ciyar da jihar gaba, kuma gamsuwa da hakan ya sanya a kusan kullum Katsinawa keta sauya sheka daga PDP zuwa APC.
Hajiya Zainab Ghana ta cigaba da cewar, a baya sun kasance a cikin Jam’iyyar PDP ne dankare wuri guda ba tare da wani cigaba ba, amma Allah cikin ikonshi daya kawo musu canji daga sama na Baba Buhari da kuma Gwamna Masari a matakin jiha, sai ya zamana gaba daya sukayi dango zuwa APC, kuma dukkanin Jama’ar jihar ta Katsina shaidu akan wannan cigaba da aka samu.
Lokacin da yake karban Matan zuwa ga Jam’iyyar APC, Gwamna Aminu Bello Masari wanda ya samu wakilcin Mataimakin shi na ayyuka na musanman Alhaji Tanimu Sada ya tabbatarwa Matan da suka canza shekan cewa, zasu samu cin gajiyar romon dimukuradiyya a jihar, ba kamar rikon sakaina da PDP tayi musu a baya ba, inda yayi fatan kafin nan da shekarar zabe ta 2019 za’a wayi gari babu wani dan PDP a jihar Katsina gaba daya.
Matan da dama da aka zanta dasu sun bayyana cewar, gamsuwa da tsari da salon shugabanci irin na Mai girma Gwamna Aminu Bello Masari ne, ya sanya suka yanke shawarar canza sheka daga PDP zuwa APC, kuma zasu cigaba da nuna goyan baya ga gwamnatin Aminu Bello Masari, tare da fatan zaiyi tazarce har sau biyu.
Daga karshen Taron Kungiyar magoya bayan Gwamna Masari mai suna “Masari Network For Continuity ” ta karrama Gwamnan da lambar yabo domin kara karfafawa gwamnatin gwiwa wajen ayyuka raya kasa da taimakon al’umma data sanya a gaba, inda Alhaji Tanimu ya amsa a madadin gwamnan
Rariya

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*