Photos: Fitaccen Dan Fim Din Hausa, Malam Waragis Na Bukatar Agajin Gaggawa

KALUBALE GA ‘YAN FIM DIN HAUSA: Fitaccen Dan Fim Din Hausa, Malam Waragis Na Bukatar Agajin Gaggawa
..yana fama da ciwon koda
…rashin kudin jinya ya sa an dawo da shi gida daga asibiti
Daga Aliyu Ahmad
Fitaccen dan fim din Hausan nan Malam Muhammad Umar wanda aka fi sani da Malam Waragis yana cikin mawuyacin hali na rashin lafiya sakamakon ciwon koda da yake fama da ita a yanzu haka. Inda bincike ya nuna cewa yanzu haka Malam Waragis ko magana ba ya iya yi, komai saidai a yi masa.
A yayin da RARIYA ta ji ta bakin dansa daya tilo da haifa, wato Ibrahim Muhammad Umar (Faradulla), ya bayyana cewa da farko an kwantar da su ne a asibitin Sunnah dake garin Jos, amma daga bisani likitoci sun nemi a canza musu asibiti zuwa inda ya kamata a yi masa wankin kodan.
Ibrahim mai kimanin shekaru 21, ya kara da cewa ” dama ni kadai nake fafutaka wajen nemo kudin jinyar mahaifina nawa, kuma yanzu haka dan jarin da nake juyawa a sana’ar kera takalma da nake yi duk ya kare, kuma yanzu ba ni da halin da za a yi masa wankin kodan kamar yadda likitoci suka bukata.
Don haka Ibrahim ya yi kira ga daukacin abokan sana’ar mahafin nasa kama daga maza da mata wadanda Allah ya hore musu da su taimaka su ceto ran mahaifin nasa.
Ibrahim ya kuma yi kira ga sauran jama’a wadanda ba ‘yan fim ba da su taimaka da dan abin da Allah ya hore musu domin ganin an yi wa mahaifin nasa magani.
Yanzu haka dai Malam Waragis yana jinya a gidansa dake Layin Gangare a garin Jos.
Ga duk mai bukatar taimakawa Malam Waragis, ga account number na dansa
BANK: First Bank
ACC Number: 3071453500
NAME:  Ibrahim Muhammad Ummar
Domin karin bayani za a iya tuntubar dan Malam Waragis, wato Ibrahim ta wannan lamba 0814 856 0384

Daga Rariya 
naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*