Boko Haran Ta Sake Sakin 82 Daga Cikin 'Yan Matan Chibok


Daga Rariya
Rahotanni sun nuna cewa kungiyar Boko Haram ta sake sakin 82 daga cikin ‘yan matan Chibok sama da 300 da ta sace a cikin watan Afrilu na shekarar 2014. Wata majiya mai tushe daga rundunar tsaro ce ta tabbatar da hakan ga najiyarmu ta Sahara Reporters.
Kamar yadda majiyar ta tabbatar, sake sakin wasu daga cikin ‘yan matan ya biyo bayan zaman sulhun da aka yi ne tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar ta Boko Haram. Saidai majiyar ba ta tabbatar da irin yarjejeniyar da aka cimmawa ba a yayin zaman har ta ga an saki ‘yan matan.
Majiyar ta kara da cewa ‘yan matan kuda 82 wadanda ba a jima da sakin su ba, yanzu haka suna garin Banki dake jihar Borno, inda suke jiran jirgi ya zo ya kwashe su zuwa wurin da ba a tabbatar ba.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*