Ana Daf Da Fara Gwabzawa Tsakanin Koriya Ta Arewa Da Amurka

Daga NAIJ HAUSA
– Koriya Ta Arewa ta ce ta sake damke wani ba-Amurke, wanda ta zarga da aikata laifi na yin karan tsaye.
– Kafar yada labaran gwamnatin Koriya ta Arewa ta, KONA, ta ce an kama Kim Hak Song ranar Asabar.
Rahoton ya ce ya taba aiki da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Pyongyang, Jami’a mai zaman kanta daya tilo a duk fadin kasar ta Koriya Ta Arewa, wadda ta ke kuma da dinbin malamai daga kasashen waje fiye da yadda aka saba gani.
NAIJ.com ta samu labari a wata takardar bayani, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce, “Kare lafiyar duk wani ba’Amurke na daya daga cikin abuwan da mu ka fi ba su muhimmanci.
Muddun aka ce an kama wani ba-Amurke a Koriya Ta Arewa, to mu kan yi aiki ne da ofishin jakadancin Swedin da ke Pyongyang wajen kubutar da shi.Kim Hak Song shi ne ba-Amurke na hudu da ke hannun Koriya Ta Arewa kuma kamun nasa ya zo ne a daidai lokacin da Amurka da Koriya Ta Arewa ke dada hararan juna saboda shirin nukiliyar Koriya Ta Arewar.
Tuni Shugaban Amurka Donald Trump ya tura wani jirgin ruwa mai dakon jiragen sama na yaki da bataliyansa daura da ruwayen na Koriya, a matsayin tauna tsakuwa game da manufofin wannan kasar mai bin tafarkin kwaminisanci.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*