Photos: An Kashe Wani Dalibi A Garin Mararraban Gurku

Daga Rariya
A ranar Juma’ar da ta gabata ne wani dalibi mai suna Muhammad Aliyu dan kimanin shekaru 23 ya gamu da ajalinsa sakamakon rikicin da ya barke tsakaninsa da wani matashi, inda ya daba masa kaho a kirji.
Lamarin wanda ya auku da misalin sha biyu na rana, majiyarmu ta rawaito cewa mamacin, wanda dalibi ne a makarantar sakandire ta Bakin Ado dake kan titin Masaka a karamar hukumar Karu ta jihar Nassarawa, ta rawaito cewa marigayin ya gamu da ajalin sa ne jim kadan da dawowarsa daga makaranta.
A yayin jin ta bakin mahaifiyar mamacin, ta bayyana cewa dan nata bai jima da barin gida bayan ya dawo daga makaranta, sai ya sake fita, cikin dan kankanin lokaci sai aka kira ta a waya cewa an raunata dan nata sakamakon fada da suka yi da wani amma an garzaya da shi asibiti.
“A lokacin da na isa asibitin ban ga dan nawa ba, sai aka sake kirana aka ce min na dawo gida an kawo gawarsa”.
A yayin da aka gayyato jami’an tsaro domin shiga lamarin, bincikensu ya kasa gano musu yadda aka yi abin ya faru, da kuma gano wanda ya yi kisan, tare da gano su waye suka kawo gawar mamacin gida, domin wasu da har zuwa yanzu ba a san ko su wanene ba, sune suka dauko gawar suka jibge a kofar gidansu mamacin, sannan abokansa suna gudun gurfana a gaban ‘yan sanda don yin bayani game da abinda suka sani kan mutuwar.
Daga bisani dai iyayen mamacin sun bar wa Allah komai, inda bayan ‘yan awanni da rasuwar dan nasu suka bukaci a yi masa jana’aiza.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*