Darikar Tijjaniyya Ta Kaddamar Da Shirin Taimakon Marayu, Ilimi Da Kiwon Lafiya

Daga Jaridar Rariya
Darikar Tijjaniya a Nijeriya ta kaddamar da wani shirin da zai taimaka mata wajen samun kudaden da zata inganta harkoin ilimi da kiwon lafiya a maimakon dogaro da gwamnatoci da kuma mika kokon bara ga dai dai kun mutane.
Shi dai wannan tsari za a rinka saida katin shigen irin wanda ake amfani dasu a wayar salula wanda da zarar mutun ya saya ya loda sai kudi ya shiga asusun darikar Tijjaniya.
A jawabinsa a wurin taron Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya yabawa wannan yunkurin na taimakon kai da kai, shima tsohon kakakin majalisar wakilai na tarayya Ghali Umar Na Abba, ya ce makasudin wannan taron shine domin wayarwa da juna kai akan alfanun gudunmawa domin taimakawa juna.
Jami’in kamfanin da ya buga katin Malam Imrana Jafaru, yace fa’idojin katin shine na samun kudaden domin magance matsalolin asibiti da na yara wadanda basu zuwa makaranta da kuma marayu har ma da mata masu bukatar tallafi.
Ya kuma kara da cewa duk wanda yake da katin rajista zai samu ragwame a asibiti ko makarantun da za a gina domin taimakawa al’uma.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*