Buhari Ya Nada Sabbin Ministoci Guda Biyu

Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya tura wa majalisar Dattawa sunayen ministoci biyu wadanda yake bukatar majalisar ta tantance su don fara aiki.
Rahotanni daga majalisar sun nuna cewa sabbin ministocin za su maye gurbin karamin Ministan Kwadago, Marigayi James Ocholi daga jihar Kogi sai kuma wanda zai maye gurbin Ministan Muhalli, Amina Mohammed wadda ta samu mukamin Mataimakiyar Sakataren Majalisar Dinkin Duniya wanda kuma tana wakiltar jihar Gombe ne.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*