Ban Yi Nadama Kan Wasikar Da Na Rubutawa Buhari Ba – El Rufa'i

Gwamnan Kaduna, Malan Nasir El Rufa’i ya jaddada cewa bai yi Nadama kan wasikar da ya rubutawa Shugaba Muhammad Buhari ba inda a cikin wasikar ya kalubalanci Shugaban kan cewa kin daukar gaggauta kan wasu muhimman batutuwa suka kara Jefa kasar nan cikin kunci.
Haka ma, Gwamnan ya caccaki Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal da kuma Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Abba Kyari inda ya bayyana cewa mutanen biyu ba su san aikinsu ba musamman yadda suke wulakanta jigogin APC, gwamnoni da ministoci.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*