Sojojin Najeriya Sun Kashe Yan Boko Haram 10

Sojojin Najeriya sun kashe wasu da ake tunanin ‘Yan Boko Haram ne da suka yi yunkurin kai hare haren kunar bakin wake a garin Maiduguri na Jihar Borno a jiya Lahadi.
Rahotannni sun ce an ji karan harbe harbe da fashe fashe a sassan birnin Maiduguri abin da ya tada hankalin jama’a.
Kakakin rundunar Sojin ta Zaman Lafiya Dole Kanal Mustapha Anka yace sojojinsu ne suka murkushe wasu da ke shirin kai harin kunar bakin wake a Ajiri da ke hanyar Damboa, da wasu wurare uku kuma kimanin 10 daga cikinsu aka kashe 10.
A sanarwar da ya fitar Kanar Anka ya bukaci mutanen yankin su kwantar da hankalinsu, domin jami’ansu na ci gaba da bincike domin tabbatar da sun zakulo sauran maharan.
Wasu rahotanni sun ce Sojojin sun yi kokarin hana wa mayakan ne shiga Maiduguri daga Kauyen Aladuwari.
Babu dai cikakken bayani akan adadin fararen hula da aka kashe a musayar wutar da aka yi tsakanin Sojojin da mayakan na Boko Haram.
A ranar Lahadi rahotanni sun ce ‘Yan Boko Haram sun shiga kauyen Jiddari Polo da safe inda suka yi ta harbe harbe.
Wannan kuma na zuwa ne a yayin da gwamnatin Najeriya ke ikirarin samun nasarar kawo karshen Boko Haram.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*