Sepp Blatter na jinya a gida

Kakakin shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA wanda aka dakatar, Sepp Blatter, ya ce shugaban yana fama da rashin lafiya.
An dakatar da Blatter mai shekaru 79, wanda ya shafe shekaru 18 yana shugabantar hukumar, tsawon kwanaki 90, gabannin matsalar karbar hanci da hukumar ta shiga.
“Likitoci na duba lafiyarsa,” in ji kakakin Blatter, Klaus Stoehlker.
Ya kara da cewa, “Yana cikin tsananin damuwa, kuma hakan na iya zamo matsala ga mutumin da ba yaro bane.”
Stoelker ya shaida wa BBC cewa Blatter na jinya a gida, amma ana kyautata zaton zai iya samun fita kafin mako mai zuwa.
‘Yan takarar bakwai ne ke fatan nasarar kujerar Blatter a zaben kungiyar da za a gudanar ranar 26 ga watan Fabrairu.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*