[Nishadi] Ashe Ni Ne!!!

Wani Babarbare ne ya je neman kudi Legas, da ya tashi dawowa gida sai ya bar irin gashin nan da yawa a kansa. Suna tafiya a mota shi da abokinsa sai suka tsaya a bakin hanya domin su yi barci. Kafin gari ya waye suna barci sai barayi suka zo suka yi masu sata, sannan kuma suka gan shi da suma duguzum, sai suka yi masa aski kwal-kwabo. Bayan gari ya waye sun tashi ke nan, ya duba dukiyarsa bai ga komai ba, ya shafa kansa ya ji babu gashi, sai ya ce wa abokinsa: “Ni ne kuwa? Abokina, don Allah kira sunana mana.” Abokin nasa ya ce: “Madu!” Shi kuwa ya zabura da karfi ya ce: “Na’am! dan Karen nan, ashe dai ni ne!”

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*