Mijin marubuciya Rahama Abdulmajid, ya rasu a Maiduguri

Mijin marubuciya Rahama Abdulmajid, ya rasu a Maiduguri
Mun samu labarin rasuwar mijin fitacciyar marubuciyar nan Rahama Abdulmajid, kana daya daga cikin sojin Nigeria dake aikin wanzar da zaman lafiya a Maiduguri, Mejo Auwal Sa’ad,
Margayi Auwal, wanda shima marubuci ne ya rasa ransa a fagen daga inda aka kaisu domin kare martabar Nigeria daga barazanar Boko Haram a Maiduguri babban birnin jihar Borno
Wani babban marubuci Ahmad G. Dabino ya shaida cewa an haifi Auwal ne a garin Dadin Kowa karamar hukumar Doguwa ta jihar Kano, a ranar 20 ga watan Fabairu shekarar 1980. Ya yi karatunsa na Firamare a Kiru, sannan ya kammala makarantar GTC Bagauda Kano a shekarar 1996, ya yi Premier Military University in Africa (Defence Academy) Inda ya sami B.e Electrical & Electronics a shekarar 2004•
Margayi Auwal Sa’ad sun yi aure da matarsa Rahama Abdulmajeed a rana 9 ko 10 ga watan Nuwamba na shekarar 2007.
Ya rasu ya bar mahaifinsa Malam Sa’adu da ‘ya’yansa Biyu Fadima da Maryam da matarsa Rahma Abdulmajeed (Ita ma an haife ne a shekarar 1980 a Agege, Legas) marubuciyar littattafan Hausa kuma shugabar Kungiyar Mace Mutum, kungiyar marubuta mata zalla.
Kafin ya rasu a lokacin aikin soja ya zauna a garin Ibadan da Lagos da Minna, sannan ya je wajen kwantar da tarzoma a kasashen Saliyo da Laberiya sannan ya dawo ya sake zama a Jaji inda daga nan ne aka tura shi Maiduguri inda a nan ne kuma ya hadu da ajalinsa ranar 10/11/2015 a matsayin mai mukamin Mejo.
A shafinsa na facebook ya rubuta wannan kalmar da manyan baki: I LOVE PEACE!!! Allahu akbar! A wajen neman zaman lafiyar kuwa ya rasa ransa.
Daga cikin littattafan da ya rubuta akwai Linzami Da Wuta kuma an buga littafin har ya shiga kasuwa, sun kuma rubuta littafi shi da matarsa Rahama, mai suna Hanji Waje, kuma yana da wasu littattafan da ya rubuta amma ba a buga su ba.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*