Ma'aikata a Nigeria sun koka kan albashi

A Najeriya, ma’aikatan gwamnatocin wasu jihohi sun fara kokawa da jinkirin samun albashin watan Oktoba har zuwa wannan lokaci.
Ma’aikatan na cewa sun shiga mawuyacin hali sakamakon jinkirin biyansu albashin.
Ma’aikatan sun ce sakamakon rashin biyansu albashin, ba sa iya biyan kudin makarantar yaransu da kuma gudanar da harkokin yau da kullun.
Suma wasu ‘yan kasuwa musanman a jihar Kano sun ce matsalar ta shafe su, inda suke cewa al’amura sun tsaya musu cak, yayin da suma masu sana’a a harabar ma’akatun gwamnati ke cewa kwantai kawai suke yi yanzu.
To sai dai wasu gwamnatocin na cewa jinkirin samun kason kudinsu daga gwamnatin tarayya da kuma koma baya a kason kudin ne ya haifar da jinkirin albashin ma’aikatan.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*