Kotu ta amince Sambo Dasuki ya fita waje nemawa kansa lafiya

Babban Kotun tarayya mai zama a Abuja ta amince da bukatar da tsohon dogarin shugaban kasa (NSA), Sambo Dasuki ya nema na fita waje duba lafiyarsa,
Da yake yanke hukuncin shara’ar a yau Talata, alkalin Kotun mai shara’a, Ademola Adeniyi ya umurci hukumomi su maidawa Mista Dasuki takardun fasfo dinsa da suka karbe saboda ya samu damar fita waje neman lafiya,
Kuma yace babu wani sharadi da aka gindaya kan wanda ake zargin dangane da wannan izini da aka bashi,
Idan dai kuna biye, Gwamnatin tarayyar Nigeria ce ta kai karar tsohon dogarin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Sambo Dasuki bayan ta sami dumbin makamai da kuma makudan kudade a gidansa,
Alkalin Kotun yace wajibi ne wanda ake karan ya maidowa Kotu takardunsa cikin sa’o’i 72 da komowarsa gida Nigeria,
Kazalika Ademola yace sai an sami wani ya sanya hannu kafin a amince “saboda idan bai dawo ba a kama wancen”
HAUSA TIMES ta samu bayani dake nuna cewa babban mai kula da Asibitin tarayya ya gabatar da wata takarda ga Kotun cewa ‘rashin lafiyar da Mista Dasuki ke fama da ita ana iya yin jinyarsa a gida Nigeria’
Amma alkalin Kotun ya yi watsi da korafin inda yace “kowane dan kasa nada zabin tsayawa Nigeria ko fita waje domin neman lafiyarsa”

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*