Kadan Daga Cikin Falalar Jumma'a

Juma‘a ita ce mafi girma a cikin ranaku
da ALLAH Madaukakin Sarki ya halitta,
ta yadda ya bawa yahudawa zabi sai
suka zabi asabar, sa‘annan Ya bawa
nasara zabi sai suka zabi lahadi, mu kuma al‘ummar Annabi Muhammadu
Sallallahu Alaihi Wasallam sai ALLAH ya
azurta mu da wannan rana ta juma‘a.
A cikin tane ALLAH Madaukakin Sarki
ya halicci babanmu Annabi ADAM (AS)
kuma a cikin wannan rana aka sauko da shi daga AL-JANNAH, kuma a cikin
irin wannan rana ALLAH Madaukakin
Sarki zai tashi alqiyama.
Hadisi ya tabbata a cikin muslim cewa
Manzon Allah Sallallahu Alaihi
Wasallam yace idan ranar juma‘a ta zo duk halittun ALLAH Madaukakin Sarki
hankalinsu a tashe yake (sabo da
tsoran kada ALLAH ya tashi qiyama a
wannan ranar). Sai mutum da al-janni
kawai hankalin su yake a kwance.
Haka kuma yana daga falalar ta juma‘a Manzon ALLAH Sallallahu Alaihi
Wasallam yace akwai wata sa‘a wanda
duk ya risketa yana mai addu‘a to
ALLAH zai karbi addu‘arsa. Muslim ne
yarawaito.
Ana son kamewa da yawaita zikiri da salatin Annabi da iyalan gidansa (a.s).
Ana son
yawaita karatun al-qur’ani da addu’o’i
ko sauraransu ta hanyar radio.
Yana daga cikin sunnar Annabi
Sallallahu Alaihi Wasallam yana karanta suratul KAHFI kowacce
juma‘a. Da dai sauran falalar ta masu
dinbin yawa.
Ya dan uwa ka kasance mai koyi ga
abubuwan shugabanmu Annabi
Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallam.
Ya ku musulmi! mu yi gasa a kan
wannan alheri mai girma, wanda Allah
ya sanya shi cikin ranar Juma’a ga
wanda ya sunnanta da sunnan
Annabi a cikin wannan, mu tsaftacce jukkunanku, mu sanya mafi kyawun
tufafin mu, mu yi asuwaki, mu sanya
turare, mu yi sammako don mu tafi
sallar Juma’a, mu lazimci ladubban
Annabi (S.A.W), da tsari na
Muhammadiyya. mu kasance daga masu rigaye zuwa alherai, masu
rabauta da mafiya daukakar darajoji,
(Wannan falala ce ta Allah da yake ba
da ita ga wanda yaso, kuma Allah shi
ne ma’abocin falala mai girma).

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*