Hukumar Kastam Zata Kori Ma'aikata 400

Hukumar Kastam na shirin koran ma’aikata 400 daga hukumar saboda, rashawa, rashin biyayya da kuma rashin zuwa aiki. Jaridar Vanguard ta ruwaito.
A ranar Juma’a 30 ga watan Oktoba, hukumar ta bada sanarwar korar ma’aikata 34. Sannan kuma a ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba, manyan mataimakan Shugaban Kastam guda 5 suka aje aikin su.
Rahotanni sun nuna cewa akwai wasu ma’aikata wadanda a wannan makon ne dama zasu aje aikin su. Shugaban hukumar sai ya basu umurnin canza wajen gudanar da aiki, amma sai suka ki bin dokar. Wasu sai suka tafi wajen yan majalisa suka nemi da su hana yin hakan.
A cewar Industry Executives, murabus din mataimakan Shugaban Kastam guda 5 zaya bada dama ayi ma wasu katin girma. Amma mataimakin shugaban Kastam, kuma jami’in hudda da jama’a na hukumar, Adewale Adeniyi, ya musanta hakan.
A Wata sabuwa, hukumar kastam ta saki hoton jirgin ta Cessna CJ4 wanda ake amfani dashi ana duba iyakar Najeriya. ministar kudi ta lokacin Jonathan, Ngozi Okonjo Iweala ce ta kaddamar da jirgin a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*