Hatsarin jirgi ya hallaka mutane 40 a Sudan ta Kudu

Wani jirgin sama ya yi hatsari a kusa da filin jiragen sama na Juba da ke Sudan ta Kudu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 40.
Wani ma’aikacin gidan rediyon Miraya da ke birnin ya ce ya kirga gawarwakin mutane arba’in a waurin da jirgin ya fadi.
Har yanzu dai babu cikakken bayani a kan yawan mutanen da ke cikin jirgin.
Gidan rediyon Miraya ya ce jirgin na daukar kaya ne wanda ke kan hanyarsa ta zuwa gundumar Paloch da ke jihar Upper Nile, kuma ya yi hatsari ne jim kadan bayan ya tashi.
Kakakin shugaban kasar, Ateny Wek Ateny ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akalla mutane biyu ne suka rayu, da wani ma’aikacin jirgin da kuma wani jariri.

naijasole

CLICK TO DROP YOUR COMMENT


Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*